‘Dan wasa Volodymyr Zelenskiy yana samun nasara a zaben Ukraine

‘Dan wasa Volodymyr Zelenskiy yana samun nasara a zaben Ukraine

Labari ya zo mana daga BBC cewa wani mai wasan barkwanci yana bada mamaki a zaben sabon shugaban kasa da ake yi a Ukraine inda sakamakon zabe su ka nuna cewa shi ne yake samun nasara.

Volodymyr Zelenskiy wanda bai taba wani aikin gwamnati ba, shi ne kan gaba a zaben shugaban kasa da ake yi a Ukraine. Kawo yanzu BBC ta rahoto cewa Volodymyr Zelenskiy ya samu kashi 30% na kuri’un da aka kada a kasar.

Shugaban kasan da ke kan mulki a halin yanzu watau Petro Poroshenko yana da kashi 16% ne kacal na kuri’un da aka tattara. Irin su tsohuwar Firayim Minista Yulia Tymoshenko, tuni dai aka yi waje da su a babban zaben na bana.

A daidai wannan lokaci da aka kididdiga fiye da kashi 50% na kuri’un da aka kada, Volodymyr Zelenskiy shi ne ke kan gaba da tazarar da ba ta isa ta bada nasara.Shiya sa Zelenskiy zai shiga zaben zagayen karshe da Petro Poroshenko.

KU KARANTA: Najeriya ce kasa ta 6 a jerin ban takaici a fadin duniya - Bincike

‘Dan wasa Volodymyr Zelenskiy yana samun nasara a zaben Ukraine
Volodymyr Zelenskiy da Petro Poroshenko za su kara a karashen zaben Ukraine
Asali: Depositphotos

Poroshenko bai ji dadin yadda aka soma tika sa da kasa ba. Ma’aikatar harkokin gidan kasar tace an samu tashin hankali a yayin gudanar da zaben. Sai dai masu sa-ido a harkar zabe sun tabbatar da cewa an yi zaben ne hankali kwance.

Zelenskiy wanda bai da wani aiki da ya wuce wasan kwaikwayo na barkwanci har ya shirya wani wasa inda aka ga wani Bawan Allah wanda ba kowa ba, ya zama shugaban kasa. Da alamu hakan na shirin faruwa a zahiri a kasar Ukraine.

BBC tace daga cikin abin da ya taimaki Zelenskiy, shi ne yadda yake jan matasan kasar da kuma kwarewar sa a harshen Rashanci da kuma yaren mutanen Ukraine. Sai dai kuma alakar sa da Igor Kolomoisky na iya jefa sa matsala.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel