Osita Okechukwu yana tare da Lawan da Gbajabiamila a Majalisa

Osita Okechukwu yana tare da Lawan da Gbajabiamila a Majalisa

Shugaban hukumar yada labarai na Najeriya, VON, Mista Osita Okechukwu, ya nuna goyon bayan sa ga wadanda jam’iyyar APC ta ke so a damkawa shugabancin majalisar tarayyar kasar a wannan karo.

Osita Okechukwu ya bayyana cewa Sanata Ahmad Lawan da kuma Honarabul Femi Gbajabiamila duk sun cancanci su rike majalisar tarayya. Okechukwu yana ganin cewa Lawan da Gbaja duk sun cancanci jan ragamar majalisa.

Mista Okechukwu wanda yana cikin manyan jam’iyyar APC yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya gana da manema labarai wajen wani taron bikin aure da aka shirya a cikin Garin Nkerifi a cikin karamar hukumar Nkanu a Enugu.

Shugaban hukumar VON ta kasar yake cewa ana sa ra’ayin, ko da APC ba ta nuna fifiko ba, Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila su na da duk abin da ake bukata wajen jagorancin majalisar dattawa da kuma majalisar wakilai.

KU KARANTA: Rikici: Ndume ya caccaki shirin APC na kakaba Lawan da karfi da yaji

Osita Okechukwu yana tare da Lawan da Gbajabiamila a Majalisa
Sanatoci na sukar matakin da APC ta dauka na zakulo Lawan
Asali: Twitter

Cif Osita Okechukwu ya kuma roki irin su Sanata Mohammed Ali Ndume da Orji Uzor Kalu da ke harin kujerar majalisar dattawan da su hakura su janye saboda irin tsayin-dakar da su Sanata Ahmad Lawan su kayi a cikin tafiyar APC.

Babban Jigon na APC a Kudu maso gabashin Najeriya ya kuma nuna cewa shugaban kasa Buhari ba zai rika juya majalisar kasar idan har Ahmad Lawan ya zama shugaban ta ba, yake cewa shugaba Buhari ya san da gashin-kan Sanatoci.

Wani Jagoran kungiyar nan ta Zikist Buharist Movement da kuma babban Sakataren kungiyar Buhari Support Organisation na yakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne su kayi aure a cikin jihar Enugu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel