Babban sufetan Yansanda ya aurar da yayansa mace da namiji a Lafiya

Babban sufetan Yansanda ya aurar da yayansa mace da namiji a Lafiya

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar ya aurar da yayansa guda biyu a karshen makon data gabata a fadar Sarkin Lafiya dake babban birnin jahar Nassarawa, garin Lafiya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban sufetan ya aurar da dansa mai suna Salmanu Mohamemd Adamu daya auri Fatima Mohammed, yayin da ya aurar da diyarsa mai suna Nafisaru Mohammed Adamu ga Ibrahim Mohammed Ubandoma.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban manajan banki da yan uwansa 2

Babban sufetan Yansanda ya aurar da yayansa mace da namiji a Lafiya
Simon Lalong, Almakura da Mohammed
Asali: UGC

Babban limamin Masallacin Lafiya, Malam Dahiru Dalhatu ne ya jagoranci daurin auren, inda kowanne daga cikin angunan biyu ya biya sadakin kudi naira dubu dari dari (N100,000) don aurar amaryarsa.

A yayin jawabin nasa, Liman Dalhatu yayi addu’ar Allah ya baiwa ma’auratan zaman lafiya mai daure, Allah Ya sanya albarka a rayuwarsu ta aure tare da soyayya da tausayin juna a tsakaninsu.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin akwai gwamnan jahar Nassarawa, Umaru Tanko Al-Makura, gwamnan jahar Filato, Simon Lalong, mataimakin gwamnan jahar Kano, Nasiru Gawuna.

Sauran sun hada da sabon gwamnan jahar Nassarawa, Injiniya Abdullahi Alhaji Sule, Sanatan George Akume, manyan sarakunan gargajiya daga ciki da wajen jahar Nassarawa, da kuma manyan baki da dama.

A wani labarin kuma, fusatattun matasa sun jefi gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa a yankin Goron Dutse na cikin birnin jahar Kano don nuna rashin amincewarsu da gwamnatinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel