Kujerar Kakakin majalisa: Duk da zabin jam'iyya, mutane 8 za suyi takara

Kujerar Kakakin majalisa: Duk da zabin jam'iyya, mutane 8 za suyi takara

Shugaban masu rinjaye a majalisa wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya alanta niyyar shiga takarar kujerar kakakin majalisar wakilan tarayya a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris, duk da cewa jam'iyyar APC ta rigaya da bayyanashi a matsayin zabinta.

Akalla sabbi da tsofin yan majalisar wakilai da suka halarci taron sun keta 110 wanda ya kunshi yan jam'iyyar APC, da yan jam'iyyun PDP, APGA, AA da APM domin nuna goyon bayansu.

A yanzu haka, Femi Gbajabiamila zai fuskanci wasu yan takara kujerar bakwai kuma da alamun ba zasu janye masa ba.

Sune mai magana da yawun majalisa, Abdulrazak Namdas (APC, Adamawa), Mukhtar Aliyu Betara (APC, Borno), Idris Wase (APC, Plateau), Umar Bago (APC, Niger), Nkeiruka Onyejeocha (APC, Abia), John Okafor (APC, Imo), Babangida Ibrahim (APC, Katsina) and Mohammed Kazaure (APC, Jigawa).

KU KARANTA: Zababbun Sanatoci sun mayarwa Tinubu Martani

Amma, wani dan majalisa ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa shugabannin jam'iyyar APC sun rigaya da zaban Femi Gbajabiamila shi yasa yan majalisa irinsu bulaliyar majalisa, Alhassan Ado Doguwa, Tahir Monguno da Khadija Bukar Abba, suka halarci taron kuma suka gabatar da jawabi.

Majiyar ta kara da cewa a wannan karon, shugaba Muhammadu Buhari ya sanya baki cikin shugabancin majalisa, kuma ya yiwa gwamnoni magana su fadawa yan majalisunsu su zabi Femi.

Yace: "Wasu gwamnoninmu sun tuntubemu. Saboda haka an yi an gama. Ba zamu iya sabawa jam'iyyar ba wannan karon."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel