Ban da kudirin razana kowa – Ganduje

Ban da kudirin razana kowa – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta da kudirin razana kowa.

Yayi alkawarin shugabanci nagartacce, cewa “Ba zan yaudari mutanen jihar ba kuma babu wanda gwamnatina za ta tozarta ko kuma ta razana.”

A wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan bayanai na jihar, Muhammad Garba, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta da kudirin kulla makirci ga kowa imma a matakin gwamnati ko kuma a wani mataki na mai zaman kansa.

Ban da kudirin razana kowa – Ganduje
Ban da kudirin razana kowa – Ganduje
Asali: Depositphotos

“Bamu da kudirin tozarta kowa imma ma’aikacin gwamnati ko wani mai zaman kansa. Zabe ya kunshi zafafan muhawara kan banbancin akidar siyasa, amma duk sun zama tarihi sannan muna da babban aiki a gabanmu na hada kai muyi aiki tare saboda Kano mallakarmu ce dukka,” inji Garba.

Yace nasarar gwamnan a zaben jihar mallakar dukkanin mutane ne ba tare da la’akari da banbancin akidar siyasa ba, don haka “tare za mu yi aiki domin ci gaban jihar.

KU KARANTA KUMA: Ba na fargabar fuskantar PDP a kotu - Ganduje

“Kano mallakarmu ce mu duka. Za mu rungumi kwa; sarakunan gargajiya, malamai, ma’aikatan gwamnati da duk sauran jam’iyyar da ke da muradi. Akwai bukatar mu hadu da dukkanin mutane don ci gaban jiharmu.” Inji shi.

Ya ce Ganduje zai ci gaba da kasancewa a matsayarsa na mutunta duk wadanda suka cancanta, cewa “gwamnan zai mika hannu ga duk wanda yazo sannan yayi aiki tare da kowa domin ci gaban jihar.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel