Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban manajan banki da yan uwansa 2

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban manajan banki da yan uwansa 2

Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da wani babban manajan bankin First Bank, Yusuf Dare tare da yan uwansa su biyu da nufin yin garkuwa dasu kamar yadda suka saba yi a jahar, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yusuf Dare, wanda shine manajan bankin First Bank dake karamar hukumar Bakura ya fada hannun miyagun tare da yan uwansa ne a ranar Asabar, 30 ga watan Maris, yayin da yan bindigan suka kai masa farmaki har gida a gidansa dake garin Gusau.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mutane 4 yan gida daya sun mutu a hadari a Bauchi

Haka zalika Yusuf, kanine ga tsohon babban daraktan bankin First Bank, kuma dan takarar gwamnan jahar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar APC , Malam Dauda Lawal Dare, kamar yadda wani dan uwansa ya tabbatar.

Da misalin karfe 9 na dare ne yan bindigan suka kai wannan farmaki gidan Yusuf, inda suka yi awon gaba da shi da yan uwannnasa guda biyu, kuma har yanzu babu wanda keda masaniyar inda suke ko halin da suke ciki, sakamakon har yanzu basu tuntubesu ba.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar Zamfara, Mohammed Shehu ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace a yanzu haka sun kara kaimi wajen gano inda mutanen suke, tare da ceto rayuwarsu daga hannun miyagun.

Daga nan muna addu'ar Allah Ya tseratar da rayuwarsu, da rayuwar duk wadanda miyagu suka yi garkuwa dasu, kuma Allah Ya kare mu da kariyarsa gaba daya, Amin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel