APC ba mallakarka ba ce: Zababbun Sanatoci sun mayarwa Tinubu Martani

APC ba mallakarka ba ce: Zababbun Sanatoci sun mayarwa Tinubu Martani

Rikicin da ya kunno wuta a cikin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kan zabin shugabannin majalisar dokokin kasa ya kara rincabewa yayinda wasu yan majalisan suka lashi takobin fito-na-fito da jam'iyyar, Jaridar Thisday ta bada rahoto.

Wasu zababbun Sanatocin jamiyyar APC sun nuna bacin ransu kan jawabin da jigon jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, yayi kan tilasta musu zaban shugaban majalisa. Sunce hakan bai kamata ya fito daga bakin jagora ba.

Wasu daga cikin zababbun Sanatocin sun gana jiya a birnin tarayya Abuja domin tattaunawa ka zabin da jam'iyyar tayi da kuma matakin da zasu dauka.

A karshen makon da ya gabata, Tinubu ya ce duk wanda bai amince da zabin jam'iyyar kan Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila ba, ya fita daga jam'iyyar.

Zababbun yan majalisan sun tunawa Tinubu cewa jam'iyyar ta kowa da kowa ce ba mallakar mutum daya ba. Yace : "Asiwaju ya tuna cewa jam'iyyu da dama suka hade domin zama APC shekaru biyar da suka gabata, saboda haka ba mallakarsa bace."

Sunce a maimakon barazanar da yake musu, gwamnda shugabannin jam'iyyar su zanna dasu kan yadda za'a zabi shugabanni na kwarai ga majalisar dokokin.

Wnai snata daga yankin Arewa maso tsakiya yace: "Har yanzu ba'a zauna damu domin tattaunawa ba kawai sai mukaji Oshiomole ya sanar da cewa Lawan jam'iyyar ta zaba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel