An jefi Gwamnan Jihar Kano Ganduje da Tawagarsa a Goron Dutse

An jefi Gwamnan Jihar Kano Ganduje da Tawagarsa a Goron Dutse

- Mun ji rade-radin cewa an jefi Tawagar Gwamna Ganduje a cikin Kano

- Shi ma Shugaban Jam’iyyar APC ya tsallake rijiya da baya a Nasarawa

- Yanzu haka APC ce ta lashe zaben Jihar Kano wanda ya bar baya da kura

Mun samu labari cewa wasu Bayin Allah sun yi wa Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano wanda ya samu zarcewa kan mulki a zaben bana ihu bayan da ya shiga Yankin Goron Dutse da ke cikin kwaryar Birnin jihar Kano kwanan nan.

Bisa dukkan alamu Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Tawagarsa sun gamu da jama’an da ba su goyon bayan su a cikin Garin Goron-Dutse. Wasu sun dauki bidiyon yadda aka rika yi wa Gwamnan da kuma mukarrabansa ihun ‘ba mu yi!’

KU KARANTA: Abba Gida-Gida ya sha alwashin karbe zaben Kano a gaban Kotu

An jefi Gwamnan Jihar Kano Ganduje da Tawagarsa a Goron Dutse
Wasu Samari sun yi wa Gwamna Ganduje ature a cikin Kano
Asali: Twitter

Kamar yadda bidiyoyin da aka saki a kafofin sadarwa na zamani su ka nuna, an ga wadannan mutane dauke da hotunan manyan ‘yan adawa na jihar Kano inda su ka rika nunawa Gwamnan na jam’iyyar APC cewa sam ba su tare da shi.

Haka zalika wani Bawan Allah ya kuma bayyana cewa shugaban jam’iyyar na jihar Kano watau Abdullahi Abbas Sanusi ya gamu da wasu Matasa da su ka rika jifar motar sa a lokacin da ya shiga wani yanki a karamar hukumar Nasarawa.

Shugaban na APC ya tafi yankin ne domin raba takardun fam ga masu bukatun wani tsarin tallafin kananan sanao’i da gwamnatin Mai Girma Abdullahi Ganduje ta kawo. A bayan nan dai gwamnatin ta dage da ayyuka a cikin Nasarawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel