Abinda aka yiwa masu garkuwa da mutane kafin su sake ni - Sheikh Sulaiman

Abinda aka yiwa masu garkuwa da mutane kafin su sake ni - Sheikh Sulaiman

Sheikh Ahmad Sulaiman, fitaccen makarancin Qura,ani, ya yi hira da kamfanin jaridar Daily Trust inda ya bayyana halin da ya shiga bayan ya shafe kwanaki 13 a hannun wasu masu garkuwa da mutane da suka sace shi a kan hayar Sheme zuwa Kankara a jihar Katsina.

Da yake amsa tambaya a kan adadin kudin da masu garkuwa da mutanen suka karba kafin su sake shi, sai Shehun malamin ya ce; "na ji an ce sun nemi miliyan N30, amma kudin da aka kawo masu basu cika.

"A daren da za a sake mu, sun zo sun umarce mu da mu gaggauta saka takalman mu, mu fito saboda sun ji labarin cewar ana shirin kawo masu hari saboda mu.

"Bayan mun isa wani wuri bisa rakiyar wasu daga cikinsu da babu nakami a hannun su, sai suka fahimci cewar mutanen da suka zo ba abokan gabar da suke tsammani bane, mutanen da suka zo da mahaifiyar shugaban masu garkuwar da suka kama mu ne domin yin musayar mu da ita.

Abinda aka yiwa masu garkuwa da mutane kafin su sake ni - Sheikh Sulaiman
Sheikh Ahmad Sulaiman
Asali: UGC

"Haka aka karbe mu; a gefe guda masu garkuwa da mutane, a daya gefen ga jami'an tsaro da suka kawo mahaifiyar shugaban wadanda suka yi garkuwa da mu, haka aka yi musayar mu da dattijuwar a gaban dakarun soji a Danmusa da ke jihar Katsina.

DUBA WANNAN: Ba na fargabar fuskantar PDP a kotu - Ganduje

"Daga baya ne mu ka fahimci cewar mahaifiyar shugaban masu garkuwar ta shafe tsawon kwanaki bakwai a hannun jami'an tsaro saboda ta ki amsa cewar dan ta'addar dan ta ne. Daga karshe dai ita ce ta zama silar samun 'yancin mu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel