Ba na fargabar fuskantar PDP a kotu - Ganduje

Ba na fargabar fuskantar PDP a kotu - Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyaa cewar a shirye ya ke domin fuskantar jam'iyyar PDP a gaban shari'a, wacce tayi ikirarin kalubalantar nasarar da ya samu a gaban kotu

Da yake magana a kauyen Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa yayin karbar dubban masoya da suka yi tururuwa domin taya shi murna, Ganduje ya ce, "kafin a gudanar da zabe na biyu da muka lashe, sun tafka magudi da sauran laifukan zabe da muka gano daga baya

"Su na son haka kabarin da za a binne su ne a ciki ba tare da sun sani ba.

"Dole yanzu a gudanar da bincike a kan kuri'un da suke ikirarin sun samu, hakan kuma zai tona asirin irin magudin da suka tafka a wasu wuraren yayin zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki."

Ba na fargabar fuskantar PDP a kotu - Ganduje
Ganduje
Asali: Twitter

Ganduje ya bayyana cewar an gudanar da zabe sahihi na adalci a zagaye na biyu, zaben da gwamnan ya ce jam'iyyar PDP ba ta samu damar yin cushe da aringizon kuri'u ba kamar yadda tayi a zaben farko.

Da yake bawa jama'a tabbacin cewar zai cigaba da gudanar da aiyukan gina Kano da ya fara a zangon sa na biyu, Ganduje ya yi tinkahon cewar: "duk wanda ya zo Kano zai shaida yadda garin ke bunkasa.

DUBA WANNAN: Tsaro: Mazauna Zamfara sun fara neman asirin tsarin kai daga mafarauta

"Zamu dora sannan mu rubanya a kan aiyukan da muke yi.

Gwamnan ya yi godiya ga dandazon jama'ar da suka zo domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zabe tare da basu tabbacin cewar gwamnatinsa zata cigaba da aiki domin mayar da Kan daya daga cikin jihohi mafi zaman lafiya a kasa.

"Muna godiya ga wadanda suka zabe mu, da wadanda basu zabe mu ba da ma wadanda basu yi zab ba gaba daya," a cewar Ganduje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel