Hukumar EFCC ta nemi tsohon Shugaban NIA Ayo Oke ta rasa

Hukumar EFCC ta nemi tsohon Shugaban NIA Ayo Oke ta rasa

Har yanzu an rasa gane inda tsohon shugaban hukumar NIA Ayodele Oke, da Mai dakin sa watau Folasade Oke, su ke ba. Hakan na zuwa ne bayan EFCC ta fara neman Ayo Oke ruwa a jallo kwanaki.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an nemi Ayodele Oke da IyalinSa an rasa bayan da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta soma binciken sa da laifin satar wasu makudan kudi a lokacin yana ofis.

A makon jiya ne EFCC ta bayyana cewa ta bazama neman Ayo Oke bayan da ya ki hallara a gaban kotu domin wanke kan sa daga zargi. Tun a cikin Watan Fubrairu ne dai kotu ta nemi Mista Ayodele Oke ya hallara gaban ta.

KU KARANTA: EFCC ta damke wasu makudan kudi a filin jirgin Najeriya

A farkon shekarar nan ne Ayo Oke ya tattara ya bar kasar nan tare da Iyalin na sa da sunan cewa bai da lafiya. Wannan ya sa EFCC ta nemi hukumar INTERPOL ta kasar Amurka ta taimaka mata wajen damke tsohon shugaban na NIA.

Sai dai kawo yanzu babu sunan Ayo Oke cikin wadanda Interpol ta ke bincike cikin mutum 6, 855 a Duniya. Daga cikin ‘Yan Najeriya da Interpol ta ke nema akwai irin Odife Ikemefuna da Iyinoluwa Victor da su kayi kaurin-suna.

Hukumar EFCC ta nemi a damke mata Mista Ayo Oke da Mai dakin ta sa a cikin Watan Mayu. EFCC tayi wannan jawabi ne ta bakin Mista Tony Orilade, wanda shi ne mukaddashin kakakin ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel