Abinda ya sa nake son zama shugaban majalisar wakilai - Gbajabiamila

Abinda ya sa nake son zama shugaban majalisar wakilai - Gbajabiamila

A wani taro da ya yi manema labarai a yau, Lahadi, shugaban majalisar wakilai, honarabul Femi Gbajabiamila, ya bayyana niyyar sa ta yin takarar kujerar kakakin majalisar wakilai.

A cewar sa, "ina takarar neman ofishin shugaban majalisar wakilai ne domin kawo hadin kai a tsakanin 'yan kasa. Ina neman kujerar kakakin majalisa domin kai aiyukan gwamnati kusa da talaka. Ina neman kujerar kakakin majalisa domin bawa shugabannin gobe horon da suke bukata domin zama shugabanni nagari.

"Ina neman wannan matsayi ne domin na yi amfani da matsayina wajen ganin dukkan 'yan Najeriya sun sharbi romon dimokradiyya ba tare da la'akari da kabila, addini ko jam'iyyar da suke goyon baya ba.

"Akwai aiyuka masu dumbin yawan da majalisa zata iya yi domin kawo canji a rayuwar 'yan kasa a bangarori da dama da suka hada da ilimi, lafiya, samar da wutar lantarki, yaki da talauci da sauran su.

Abinda ya sa nake son zama shugaban majalisar wakilai - Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila
Asali: UGC

"Na yi imanin cewar shugabancin majalisa mai ma'ana zai kawo gagarumin canji a matsalolin da suka dabaibaye kasar nan."

A cigaba da siyasar da ake buga wa a zauren majalisar ta wakilai, Legit.ng ta kawo maku labarin cewar sabbin mambobin majalisar wakilai da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar APC daga yankin arewa maso yamma sun ce sun saka Kawu Sumaila a gaba domin karbar duk kujerar da uwar jam'iyya ta yanke mika wa yankin da suka fito.

DUBA WANNAN: Shugabancin majalisar wakilai: Abin da ya sa muke goyon bayan Gbajabiamila - Mambobin PDP

Mambobin sun bayya cewar Kawu zasu goyi baya koda uwar jam'iyya ta yanke shawara mika shugaban majalisar zuwa yankin arewa maso yamma.

'Yan majalisar sun kara da cewa Honarabul Kawu Sumaila, mamba mai wakiltar mazabar Sumaila da Takai, ne zabin su a kan duk kujerar da jam'iyyar APC ta yanke shawarar bawa yankin Arewa maso yamma.

Ana rade-radin cewar jam'iyyar APC na shirin mika kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilai zuwa yankin arewa maso yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel