Gwamna Ugwuanyi zai ba wanda ke da labarin kisan Amadi kyautar kudi

Gwamna Ugwuanyi zai ba wanda ke da labarin kisan Amadi kyautar kudi

Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya tabbatar da tausayin sa a game da kisan wata ma’aikaciyar asibiti da aka yi kwanan nan. An rahoto cewa Ifeanyi Ugwuanyi ya sa kyautar kudi ga wanda ya kawo masa labarin wannan kisan da aka yi.

Jaridar Premium Times tace Ifeanyi Ugwuanyi yayi alkawarin raba Naira Miliyan 5 ga duk wanda ya kawo masa bayani a kan wadanda su ka kashe Maria Amadi. Amadi tayi aiki ne a babban asibitin mahaukata da ke jihar Enugu.

Ugwuanyi yayi wannan alkawari ne sa’ilin da ya gana da kungiyar Ungonzoma da sauran Malaman asbitin da ke cikin jihar Enugu. Gwamnan yace zai bada wannan kudi nan take ga duk wanda ya fada masa labarin Makasan Amadi.

KU KARANTA: Boko Haram: Magu ya gano Kungiyoyi a Borno da ke safarar Miliyoyi

Gwamnan yace Rundunar ‘yan sandan Najeriya na jihar Enugu za su bada wannan ganima ga duk wanda yake da labarin yadda aka kashe Dr. Maria Amadi. Kwamishinan ‘yan sanda Suleiman Balarabe yayi alwashin gano Makasan.

Kafin nan dama dai gwamnan yace ba zai kyale wadanda su ka kashe wannan Baiwar Allah su sha a banza ba. Gwamnan ya kuma ce za a bankado wanda su ka kashe Sakataren karamar hukumar Uzo-Uwani watau Nnamdi Peter Ogueche.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel