Siyasar majalisa: A bawa Kawu Sumaila kason yankin mu - Mambobin arewa maso yamma

Siyasar majalisa: A bawa Kawu Sumaila kason yankin mu - Mambobin arewa maso yamma

Sabbin mambobin majalisar wakilai da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar APC daga yankin arewa maso yamma sun ce sun saka Kawu Sumaila a gaba domin karbar duk kujerar da uwar jam'iyya ta yanke mika wa yankin da suka fito.

Mambobin sun bayya cewar Kawu zasu goyi baya koda uwar jam'iyya ta yanke shawara mika shugaban majalisar zuwa yankin arewa maso yamma.

'Yan majalisar sun kara da cewa Honarabul Kawu Sumaila, mamba mai wakiltar mazabar Sumaila da Takai, ne zabin su a kan duk kujerar da jam'iyyar APC ta yanke shawarar bawa yankin Arewa maso yamma.

Ana rade-radin cewar jam'iyyar APC na shirin mika kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilai zuwa yankin arewa maso yamma.

Siyasar majalisa: A bawa Kawu Sumaila kason yankin mu - Mambobin arewa maso yamma
Kawu Sumaila
Asali: Depositphotos

Sabbin mambobin na goyon bayan Kawu ne ganin cewar yana daya daga cikin su duk da kasancewar wannan ba shine karon sa na farko na zuwa majalisar wakilai ba.

DUBA WANNAN: Shugabancin majalisar wakilai: Abin da ya sa muke goyon bayan Gbajabiamila - Mambobin PDP

Jagoran sabbin mambobin, Ibrahim Al-Mustapha, ya shaidawa manema a garin Kaduna cewar sun yanke shawarar goyon bayan Kawu ne saboda gogewar sa a harkokin a suka shafi majalisa.

A cewar sa, "sabbin mambobin majalisar wakilai daga yankin arewa maso yamma na goyon bayan Kawu Sumaila a matsayin zai hau duk kujerar da uwar jam'iyya APC ta yanke shawarar bawa yankin arewa maso yamma.

"Muna goyon bayan a kan kowanne mukami uwar jam'iyya ta wullo yankin arewa maso yamma."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel