Shugabancin majalisar wakilai: Abin da ya sa muke goyon bayan Gbajabiamila - Mambobin PDP

Shugabancin majalisar wakilai: Abin da ya sa muke goyon bayan Gbajabiamila - Mambobin PDP

Wasu mambobin majalisar wakilai biyu da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar hamayya ta PDP sun fito fili sun bayyana goyon bayan su ga Femi Gbajabiamila a takarar neman shugabancin majalisar wakilai da yake yi.

Wole Oke, mamba mai wailtar mazabar Oriade/Obokun da ke jihar Osun, da Jerry Alagbaso, mamba mai wakiltar mazabar Orlu/Oru ta Gabas/Orsu da ke jihar Imo, sun bayyana cewar Gbjabiamila ne zabin mu.

Sun bayyana hakan ne a yau, Lahadi, yayin kaddamar da takarar Gbajabiamila a matsayin dcan takarar shugaban majlisar wakilai.

Da yake bayyana ra'ayin sa, Honarabul Oke ya ce babu dan takarar shugabancin majalisar wakilai da ya fi Gbjabiamila cancanta.

"Sau biyu Gbajabiamila yana ziyarta ta har gida domin sanar da ni burin sa na son yin takarar shugaancin majalisar wakilai, ya bani girma na kuma hakan ne ma yasa na halarci taron kaddamar da takarar sa.

Shugabancin majalisar wakilai: Abin da ya sa muke goyon bayan Gbajabiamila - Mambobin PDP
Femi Gbajabiamila
Asali: UGC

"In dai maganar kishi da kare mutuncin kasa ake yi, ban ga wani dan takara da ya fi Gabajabiamila cancanta ya zama shugaban majalisar wakilai ba.

"Kwararren lauya ne da ya fuskanci dokokin majalisa bayan kasancewar sa masanin doka, sannan bayan haka mutum ne mai saukin kai.

DUBA WANNAN: Rashin adalci a aikin dan sanda da siyasa: Na yi gudun gara na tarar da zago - Sanata Misau

"Ni da shi mun fito daga yanki daya kuma shine ya fi cancanta mu goya wa baya domin bawa kasa gudunmawa da irin mutane masu hazaka da basira da yankin kud maso yamma ke da su. Yanzu ina magana ne a matsayina na Honarabul Wole Oke," a cewar dan majalisa Oke da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

A nasa bangaren, Honarabul Alagabaso ya bayyana cewar yana da yakinin Gbajabiamila zai yi aiki tare da mambobin jam'iyyar adawa da basu da rinjaye a majalisar.

A kalla ya zuwa yanzu mambobi 12 daga jam'iyyar APC sun bayyana sha'awar su ta yin takarar kujerar shugabancin majalisar wakilai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel