Majalisar tarayya ta 9: Gbajabiamila ya tsaya takarar kujerar kakakin majalisa

Majalisar tarayya ta 9: Gbajabiamila ya tsaya takarar kujerar kakakin majalisa

Rahotanni daga Transcopr Hilton, Abuja na nuni da cewa Femi Gbajabiamila (APC, Lagos) ya kaddamar da yakin zaben kujerar kakakin majalisar wakilan tarayya a majalisar tarayya ta 9 da za a rantsar kasa da watanni biyu masu zuwa.

Wannan kuwa ya faru duk da cewa jam'iyyar APC wacce ke da mafi rinjaye a majalisar dattijai da majalisar wakilan tarayya ba ta kai ga raba mukamin lamba na hudu a Nigeria ma kowanne sashe na kasar ba.

Da ya ke kaddamar da yakin zabensa a fili, dan majalisar wanda ya ke cikin majalisar tsawon mulki hudu, zai shiga cikin sahun 'yan majalisu 16 da suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar kujerar mafi girma a majalisar wakilai ta tarayyar.

KARANTA WANNAN: Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un: Manoma 10 sun mutu a sabon harin Zamfara

Majalisar tarayya ta 9: Gbajabiamila ya tsaya takarar kujerar kakakin majalisa
Majalisar tarayya ta 9: Gbajabiamila ya tsaya takarar kujerar kakakin majalisa
Asali: UGC

Haka zalika zai kasance dan takara tilo daga shiyyar Kudu, da ya hada da Kudu maso Gabas, Kudu maso Yamma da kuma Kudu maso Kudu, da ya fito fili ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takara.

A jawabin da ya gabatar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Gbajabiamila ya lissafa nasabarsa da kuma matakin iliminsa, kwarewarsa da ya sa har ya ke neman maye gurbin kakakin majalisar wakilan tarayyar na yanzu, Yakubu Dogara (PDP, Bauchi).

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel