Miyagun laifuka: Kotu ta yanke wa mutane 4 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Asaba

Miyagun laifuka: Kotu ta yanke wa mutane 4 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Asaba

Wata babbar kotun jihar Delta da ke zaman ta Asaba, babban birnin jihar, ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da aikata miyagun laifuka da suka da da fashi da makami, garkuwa da mutane da kwacen mota.

Kotun ta yanke hukuncin ne a cikin wani jawabi na tsawon sa'a hudu da alkalin kotun, Jastis Flora Azinge, ya karanta a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris. Alkalin ya zartar da hukuncin ne a kan hudu daga cikin masu laifin da aka gurfanar a gaban sa.

Ana tuhumar mutanen biyar; Uche Uzondu, Emeka Amukali, Paul Egwom, Festus Oghali, da David Mario, da hada baki tare da aikata laifin fashi da makami da garkuwa da mutane.

Mai shari'a Azinge ya ware David Mario, daya daga cikin mutanen hudu da aka gurfanar saboda rashin hujja mai kwari da ta alakanta shi da laifuka da ake zargin su da aikata wa.

Miyagun laifuka: Kotu ta yanke wa mutane 4 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Asaba
Kotu ta yanke wa mutane 4 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Asaba
Asali: Twitter

A hukuncin ta, kotun ta bayyana cewar gwamnati ta kawar da wani shakku a kan mutane hudu da ta gurfanar a gaban kotun domin a yanke masu hukunci.

Kotun ta ce ta gamsu cewar hudu daga cikin wadanda ake tuhumar suna hada baki ne domin aikatu miyagun laifukan.

DUBA WANNAN: Rundunar MNJTF ta kashe mayakan Boko Haram 5, ta kama 3

Asirin masu laifin ya fara tonuwa ne bayan wani mutum da suka taba kwace wa mota ya sanar da rundunar 'yan sanda rahoton ganin motar sa a kan hanyar Asaba zuwa Benin har an canja mata fenti.

Kwamishinan shari'a na jihar Delta, Peter Mrakpor, wanda Ernes Edomwonyi, darektan sashen gurfanar da masu laifi a ma'aikatar shari'a ya wakilta, ya ce sun yi maraba da hukuncin kotun domin zai sama wa jama'a sauki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel