Da zafinsa: Gbajabiamila ne ya fi cancanta ya zama kakakin majalisar wakilai - Abdulmumin Jibrin

Da zafinsa: Gbajabiamila ne ya fi cancanta ya zama kakakin majalisar wakilai - Abdulmumin Jibrin

- Hon. AbdulmuminJibrin ya ce Femi Gbajabiamila ne kawai ya fi cancanta ya zama kakakin majalisar wakilan tarayya a majaisar tarayyar ta 9

- Jirbin ya bayyana hakan a yayin da Gbajabiamila ke bayyana kudirinsa na tsayawa takarar kujerar majalisar wakilan tarayyar a Abuja

- Dan majalisar ya kara da cewa dan majalisar da ya fito daga jihar Legas ya samu kwarewar wakilci da ake bukata, da kuma zarce sauran 'yan majalisar

Mamba a majalisar wakilan tarayya daga jihar Kano kuma shugaban kwamitin harkokin zirga zirga, AbdulmuminJibrin ya ce Femi Gbajabiamila ne kawai ya fi cancanta ya zama kakakin majalisar wakilan tarayya a majaisar tarayyar ta 9.

Jirbin ya bayyana hakan a ranar Lahadi a yayin da Gbajabiamila ke bayyana kudirinsa na tsayawa takarar kujerar majalisar wakilan tarayyar a Transcorp Hilton, Abuja.

KARANTA WANNAN: Majalisar dattijai ta 9: Ta mu ba irin ta su ba ce - Sanata Ahmed Lawan

Babban daraktan yakin zaben Femi Gbajabiamila a kujerar kakakin majalisar, ya kara da cewa dan majalisar da ya fito daga jihar Legas ya samu kwarewar wakilci da ake bukata, da kuma zarce sauran 'yan majalisar.

"Shi ne dan takarar da ya fi kowa dacewa, idan ka dauke shi to kamar an gama aikin ne. Zai kuma tabbatar da cewa majalisar wakilan tarayyar ta tsaya da kafafunta," a cewar Jibrin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel