Majalisar dattijai ta 9: Ta mu ba irin ta su ba ce - Sanata Ahmed Lawan

Majalisar dattijai ta 9: Ta mu ba irin ta su ba ce - Sanata Ahmed Lawan

- Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana irin salon da zai dauka wajen tafiyar da majalisar dattijai idan har aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar

- Mr Lawan ya ce manufarsa shi ne samar da majalisar tarayya da za ta yiwa 'yan Nigeria aiki, kuma duk wani lamari da ke da muhimmanci ga jama'a zasu bashi fifiko

- Shugaban masu rinjayen ya ce a bangarensu na majalisar tarayya, za su samar da kyakkyawan yanayin da gwamnatin kasar za ta gudanar da ayyukanta

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, a zantawarsa da manema labarai a Legas, ya bayyana irin salon da zai dauka wajen tafiyar da majalisar dattijai idan har aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar.

Mr Lawan ya ce manufarsa shi ne samar da majalisar tarayya da za ta yiwa 'yan Nigeria aiki, "Jama'a sun kara dora yakininsu akan shugaban kasa Buhari da jam'iyyar APC inda har suka zabe su a karo na biyu. Duk wani lamari da ke da muhimmanci ga jama'a muma zamu bashi fifiko.

"Zamu ci gaba da cika alkawuran da shugaban kasa da jam'iyyyarmu suka dauka a wajen yakin zabe, da suka shafi samar da ayyukan yi, farfado da tattalin arziki da kuma uwa uba magance matsalar tsaro," a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Ba zamu iya gudanar da sabon zabe a Rivers ba - INEC ta ba jam'iyyu hakuri

Majalisar dattijai ta 9: Ta mu ba irin ta su ba ce - Sanata Ahmed Lawan
Majalisar dattijai ta 9: Ta mu ba irin ta su ba ce - Sanata Ahmed Lawan
Asali: Twitter

Shugaban masu rinjayen ya ce a bangarensu na majalisar tarayya, za su samar da kyakkyawan yanayin da gwamnatin kasar za ta gudanar da ayyukanta, yana mai cewa "zamu sa ido mu tabbata gwamnatin ba ta sauka daga kan hanya ba.

"Ina son ganin kyakkyawar alaka tsakanin majalisar tarayya da gwamnati ta yadda za a samu saukin gudanarwa al'umma ayyukan ci gaba. A duk lokacin da muka samu sabani, to zamu zauna mu tattauna domin nemo hanyar warware sabanin ta yadda hakan ba zai shafi ra'ayin jama'a ba.

"Zamu tabbata mun tallafawa ayyukan majalisar zartaswa, sai dai ni ban yarda da yin fada kowanne lokaci ba. Kuma ba wai hakan na nufin cewa ba zamu juya baya ga dokokin da suka sabawa ra'ayin jama'a da kasa ba, a'a, zanso dai a samu kyakkyawar alakar aiki saboda da hakane kadai za a cimma gaci. Rikici tsakanin majalisae tarayya da majalisar zartaswa zai haddasa fitina ne ga jama'a.

"Muna kan nazarin hanyoyin da zamu magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta. Mun fara da garambawul wa dokar 'yan sanda. Kuma muna kokarin yin garambawul wa tsarin albashin fannin shari'a domin ganin suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata."

Sahata Ahmed Lawan, ya bada tabbacin cewa idan har aka bashi dama, majalisar tarayya ta 9 za ta zarce ta 8.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel