Rundunar MNJTF ta kashe mayakan Boko Haram 5, ta kama 3

Rundunar MNJTF ta kashe mayakan Boko Haram 5, ta kama 3

Rundunar sojin hadin gwuiwa ta kasashen gefen tekun Chadi (MNJTF) da hadin gwuiwar rundunar soji ta kasa ta sanar da cewar ta kashe mayakan kungiyar Boko Haram biyar a jihar Borno.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar MNJTF, Timothy Antigha, ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya fitar a birnin N'Djamena na kasar Chadi, ya bayyana cewar sojoji sun kama wasu mayakan uku yayin da wasu uku suka mika wuya ga rundunar sojoji ta kasar Kamaru.

"Rundunar sojin MNJTF da hadin gwuiwar kuma rundunar soji da ke aiki a yankin Doro Naira da Ngolon sun fafata da mayakan kungiyar Boko Haram wanda a karshe mun samu nasarar kashe biyar daga cikin su, mun kama uku, ragowar sun tsere," a cewar Atingha.

Sannan ya cigaba da cewa, "biyu daga cikin ukun da muka kama sun mutu bayan motar da suke ciki ta tarwatse bayan ta taka wani bam da 'yan Boko Haram suka binne a gefen hanya.

Rundunar MNJTF ta kashe mayakan Boko Haram 5, ta kama 3
Rundunar MNJTF
Asali: Twitter

Rundunar MNJTF ta kashe mayakan Boko Haram 5, ta kama 3
Rundunar MNJTF ta kashe mayakan Boko Haram 5, ta kama 3
Asali: Twitter

Rundunar MNJTF ta kashe mayakan Boko Haram 5, ta kama 3
Rundunar MNJTF ta kashe mayakan Boko Haram a Borno
Asali: Twitter

"Wasu mayakan uku da suka gaji da yaki ba nasara, sun mika wuya ga rundunar MNJTF ta daya dake Balgaram a jamhuriyar Kamaru.

Atingha ya ce rundunar MNJTF a shirye take domin kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram, sannan ya kara da cewa sun kassara kungiyar ta hanyar lalata makaman su da kashe mayakan su a 'yan kwanakin baya bayan nan.

DUBA WANNAN: Zargin magudi: Za mu karbi kujerar mu a Kotu - APC ta fada wa Tambuwal

Ya kara da cewa rundunar ta kai hare-hare a kan mayakan kungiyar Boko Haram a yankunan Chadi, Najeriya, da janhuriyar Nijar.

Daga cikin makaman da aka kwace daga hannun mayakan akwai wasu alburusai na musamman masu yawa da mayakan suka gudu suka bari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel