Ba zamu iya gudanar da sabon zabe a Rivers ba - INEC ta ba jam'iyyu hakuri

Ba zamu iya gudanar da sabon zabe a Rivers ba - INEC ta ba jam'iyyu hakuri

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ba za ta gudanar da wani sabon zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki a jihar Rivers ba

- Hukumar a wani taron a Fatakwal, ta sanya ranar 2 ga watan Afrelu, 2019 ta zamo ranar ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar

- Gwamna Wike ya bukaci hukumar da ta wallafa sunayen jami'an tsaron da za a girke su a cibiyar tattara sakamakon zaben domin dakile duk wani cikas da ka iya tasowa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ba za ta gudanar da wani sabon zaben gwamnoni da na 'yan majalisun dokoki a jihar Rivers ba.

Wannan ya biyo bayan ficewar dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar AAC, Biokpomabo Awara daga taron masu ruwa da tsaki da INEC ta shirya domin ci gaba da zaben jihar da ta dakatar a ranar 9 ga watan Maris.

Su ma dai yan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar SDP da LP sun fice daga taron da aka gudanar a wani dakin taro da ke hanyar 'Eastern Bye-Pass', a garin Fatakwal.

Da ya ke jawabi a wajen taron, kwamishinan INEC na kasa mai kula da jihohin Bayelsa, Rivers da Edo, May Agbamuche-Mbu, ya jaddada cewa hukumar ba za ta iya gudanar da sabon zabe a jihar ba.

KARANTA WANNAN: Kar mu yaudari kanmu - Buhari ya ce har yanzu Nigeria ba ta iya ciyar da kanta

Ba zamu iya gudanar da sabon zabe a Rivers ba - INEC ta ba jam'iyyu hakuri
Ba zamu iya gudanar da sabon zabe a Rivers ba - INEC ta ba jam'iyyu hakuri
Asali: Getty Images

Agbamuche-Mbu, wanda ya bayyana cewa hukumar za ta dawo da ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar Rivers a ranar 2 ga watan Afrelu, 2019, ya ce makasudin taro shi ne tunasar da masu ruwa da tsaki kan shirye shiryen da hukumar ta yi.

A na shi jawabin a wajen taron, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, wanda ya karyata jita jitar da ake yadawa na cewar jihar na cikin rikici, ya kuma bukaci da kar a tsoma jami'an tsaro a yayin zaben domin tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali.

Wike ya bukaci hukumar da ta wallafa sunayen jami'an tsaron da za a girke su a cibiyar tattara sakamakon zaben domin dakile duk wani cikas da ka iya tasowa..

Shima da ya ke jawabi kwamishinan 'yan sanda na jihar, Usman Balel, wanda ya bada tabbacin rundunar 'yan sanda na samar da tsaro ga jama'a ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsakin da su yi riko da zaman lafiya da kuma karbar sakamakon zaben.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel