Yunkurin kakaba Shugbannin Majalisa ba zai kai ko ina ba – Inji Ndume

Yunkurin kakaba Shugbannin Majalisa ba zai kai ko ina ba – Inji Ndume

Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Mazabar Borno a Majalisa ya bayyana cewa matakin da jam’iyyar sa ta dauka na zakulo Ahmad Lawan, zabi ne kurum na jam’iyya ba wai an nada sa bane.

Babban‘Dan majalisar wanda yake neman takarar kujerar majalisar dattawa yayi kira ga ‘Yan uwan sa da kuma jam’iyyar APC cewa su bi tsarin mulki da dokar Najeriya wajen zaben wadanda za su rike ragamar majalisa a wannan karo.

Sanatan yayi wannan bayani ne lokacin da yayi hira da Jaridar Nigerian Tribune. Ali Ndume ya gargadi APC ta gujewa afkawa cikin irin rikicin da ta shiga a 2015. Ndume yace jam’iyyar APC ta sabawa tsarin mulki wajen zabin da tayi kwana nan.

Ahmad Lawan yace abin da dokar kasa tace shi ne ‘Yan majalisa za su zabi shugaba da kuma mataimakin sa da su ke so. A dalilin haka ne Sanatan yace zai yi takarar shugaban majalisar dattawa tare da Lawan domin ya jarraba sa’ar sa.

KU KARANTA: An hurowa Saraki da Dogara wuta daf da karshen wa’adin su

Yunkurin kakaba Shugbannin Majalisa ba zai kai ko ina ba – Inji Ndume
Sanata Ndume yace dokar Najeriya ba ta hana sa takara a majalisar dattawa ba
Asali: Facebook

Sanatan na jihar Borno yace matakin da APC ta dauka na zakulo Ahmad Lawan a matsayin ‘dan takarar ta, ya ba su mamaki. Ndume yake ganin kamata yayi ace APC ta zauna da ‘yan majalisar yankin domin su fito da duk wanda su ke so.

Ndume ya nuna cewa duk wani kokarin kakabawa Sanatoci wanda ba su so kamar yadda aka yi a 1999 ba zai kai ga ci ba. Sanatan yace irin haka ne ya sa duk da ta’adin PDP ta rika kasa yankin da za su fitar da shugaba a majalisa tun 2007.

Tun kwanaki dai Sanatan mai wakiltar mazabar jihar Borno ta kudu, Ali Ndume, ya nuna cewa bai amince da matakin jam'iyyar APC na cewa Sanata Ahmed Lawan ne zai gaji Bukola Saraki ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel