Bayan zabe: INEC ta kammala shirin soke wasu jam'iyyu

Bayan zabe: INEC ta kammala shirin soke wasu jam'iyyu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kamma shirin soke wasu daga cikin dumbin jam'iyyun kasar nan da suka kasa tabuka wani abun kirki a zabukan shekarar 2019 tare da fara binciken manyan jam'iyyun kasar a kan hanyoyin da suka samu kudin yakin neman zabe da yadda suka kashe su.

Festus Okoye, kwamishinan INEC na yada labarai da wayar da kan masu zabe, ne ya sanar da hakan a Abuja yayin ganawa da manema labarai Abuja, ya bayyana cewar INEC za ta yi hakan ne da zarar an kammala ragowar zabukan da suka rage da kuma shari'o'in korafi a kan zabe da ke gaban kotu.

"Akwai hanyoyi na musamman da INEC ke amfani da su wajen binciken hanyoyin da jam'iyyu ke samun kudi da kuma yadda su ke kashe su. INEC za ta sake tsari a kan yadda jam'iyyu ke samun kudi da zarar an kammala harkokin zabe baki daya," a cewar Okoye.

Bayan zabe: INEC ta kammala shirin soke wasu jam'iyyu
Shugaban INEC; Farfesa Mahmoud Yakubu
Asali: Instagram

Kwamishinan ya koka a kan yadda wasu manyan mutane a kasar nan ke kokarin kawo wa cikas a shirin ta na gudanar da sahihin zabe a Najeriya.

DUBA WANNAN: Karin kudin haraji: Tinubu ya gargadi gwamnatin tarayya

Da yake kare INEC a kan rashin kammala zabe a wasu jihohi, Okoye ya ce, "lokacin magudin zabe ya wuce, an wuce zamanin da wani mutum zai rubuta sakamakon zabe kuma a sanar da shi. Batun rashin kammala zabe a wasu jihohi cigaba ne da hukumar INEC ta samu, bukatar son gudanar da zabe sahihi da kowa zai gamsu da shi ne ya jawo hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel