Kar mu yaudari kanmu - Buhari ya ce har yanzu Nigeria ba ta iya ciyar da kanta

Kar mu yaudari kanmu - Buhari ya ce har yanzu Nigeria ba ta iya ciyar da kanta

- Shugaban Buhari ya ce har yanzu Nigeria na fuskantar kalubale ta fuskar ciyar da kanta da kuma samawa kamfanoni kayan aiki ta hanyar noma

- Buhari ya kuma ce kalubalan har yanzu yana nan duk da cewa noma na taimakawa da kashi 25.5 wajen bunkasar tattalin arzikin kasar

- Shugaban kasar ya bayyana cewa kulla hadaka tsakanin noma da masana'antu shi zai cike gibin da ake samu na karancin abinci da kayayyakin masarufi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce har yanzu Nigeria na fuskantar kalubale ta fuskar ciyar da kanta da kuma samawa kamfanoni kayan aiki ta hanyar noma.

Buhari wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar a bukin bude baje koli na kasa da kasa karo na 40 a Kaduna, ya kuma ce kalubalan har yanzu yana nan duk da cewa noma na taimakawa da kashi 25.5 wajen bunkasar tattalin arzikin kasar.

Bukin baje koli na kasa da kasa da ake gudanarwa kowacce shekara yana gudana ne har tsawon kwanaki 10 karkashin cibiyar masana'antu, albarkatun kasa da noma ta jihar Kaduna (KADCCIMA), inda ake baje kolin sanao'i da fasahohi na cikin gida Nigeria da ma kasashen waje.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria sun lissafa abubuwan da za su tuna da Saraki bayan karewar wa'adin wakilcinsa

Kar mu yaudari kanmu - Buhari ya ce har yanzu Nigeria ba ta iya ciyar da kanta
Kar mu yaudari kanmu - Buhari ya ce har yanzu Nigeria ba ta iya ciyar da kanta
Asali: Twitter

Da ya samu wakilcin ministan masana'antu, kasuwanci da sa hannun jari, Dr Okechukwu Enelama, shugaban kasar ya bayyana cewa kulla hadaka tsakanin noma da masana'antu shi zai cike gibin da ake samu na karancin abinci da kayayyakin masarufi.

A cewar shugaban kasar, "Nigeria na ci gaba da fuskantar matsalar cimma bukatun 'yan Nigeria ta fuskar abinci, da kuma kayayyakin da masana'antu ke bukata domin gudanar da ayyukansu."

A jawabin da ya gabatar, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, yayin jinjinawa KADCCIMA bisa namijin kokarinsu na gudanar da baje kolin har na tsawon shekaru 40, ya kuma basu tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da bunkasa rayuwar jama'a ta hanyar basu tallafin horo kan sana'o'in dogaro da kai.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel