Hatsarin Jirgi: Da ace na mutu da masu bani kariya sun shiga tsaka mai wuya - Osinbajo

Hatsarin Jirgi: Da ace na mutu da masu bani kariya sun shiga tsaka mai wuya - Osinbajo

Biyo bayan hatsarin jirgin sama da ya ritsa da shi a ranar 2 ga watan Fabrairu, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce tuni da masu rataye da nauyin ba shi kariya da tsaro sun shiga cikin tsaka mai wuya da ta kasance ajali ya katse masa hanzari.

Mataimakin shugaban kasa tare da tawagar sa sun tsallake rijiya da baya yayin da jirgin da ke dauke da su mai saukar angulu ya kife a garin Kaabaa na jihar Kogi a sa'ilin da ya ke shawagi na ci gaba da tumke damara ta yakin neman zabe.

Hatsarin Jirgi: Da ace na mutu da masu bani kariya sun shiga tsaka mai wuya - Osinbajo
Hatsarin Jirgi: Da ace na mutu da masu bani kariya sun shiga tsaka mai wuya - Osinbajo
Asali: UGC

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ba bu ko kwarzane da Mista Osinbajo tare da tawagar suka samu inda daga bisani ya ci gaba da sabgar da ke gaban sa da ta sanya yayi tattaki daga garin Abuja zuwa jihar Kogi.

Cikin babbar Cocin fadar shugaban kasa, Farfesa Osinbajo ya furucin haka yayin gudanar da addu'o'I na murna a ranar Lahadi sakamakon samun nasarar tazarce ta shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KARANTA KUMA: Za mu fadada shirin N-Power - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa ya ce da tuni gwamnatin jihar Kogi ta shiga cikin tsaka mai wuya da ajali ya katse masa hanzari yayin aukuwar hatsarin da ya auna arziki na tsallake rijiya baya kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel