Za mu fadada shirin N-Power - Osinbajo

Za mu fadada shirin N-Power - Osinbajo

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin shekaru hudu a wa'adin ta na biyu za ta fadada shirin N-Power, ciyar da daliban makaranta, TraderMoni, da sauran shirye-shirye na samar da madogara bayar da tallafi ga al'umma.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin jawaban sa yayin halartar bikin murnar cikar tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, shekaru 67 a duniya da aka gudanar cikin birnin Abuja a ranar Alhamis.

Za mu fadada shirin N-Power - Osinbajo
Za mu fadada shirin N-Power - Osinbajo
Asali: UGC

Farfesa Osinbajo ya ce ko shakka ba bu gwamnatin su yayin tabbatar da kudirin ta na matakin gaba watau Next Level, za ta fadada duk wasu shirye-shiryen bayar da tallafi a zamantakewar al'ummar kasar nan musamman a fannin noma da kuma ciyar wa.

A sanadiyar amintaccen jagoranci na shugaban kasa Buhari, Farfesa Osinbajo ya ce gwamnatin su ta yi tanadin muhimman tsare-tsare da na ci gaban kasa ba bu makamantan su a duk ilahirin nahiyyar Afirka.

KARANTA KUMA: Dakarun Sojin Najeriya sun kashe Kwamandan Boko Haram da Mayakan sa 15 a Tafkin Chad

Mataimakin shugaban kasar ya kushe gwamnatin baya a sakamakon yadda kasar nan ba ta taka wani mataki na ci gaba ba duk da irin dukumar dukiya da ta yi tanadi da ba a taba samun makamancin ta ba a tarihi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel