Yan Nigeria sun lissafa abubuwan da za su tuna da Saraki bayan karewar wa'adin wakilcinsa

Yan Nigeria sun lissafa abubuwan da za su tuna da Saraki bayan karewar wa'adin wakilcinsa

Bayan shan kasa a hannun dan takarar jam'iyyar APC, Ibrahim Olorigbe, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki ba zai koma majalisar tarayya ta tara ba. Tambayar da take yawo akan kowanne dan Nigeria ita ce; Da me al'umma za su tuna da Saraki bayan karewar wa'adin wakilci da shugabancin majalisar dattijai?

Watanni kadan gabanin karewar wa'adin wakilcinsa da kuma shugabancin majalisar dattijan, 'yan Nigeria a kafofin sada zumunta na yanar gizo wun tafka muhawara akan abubuwan da suke ganin za a tuna da Saraki ko bayan saukarsa.

Yayin da wasu ke jinjina masa a matsayinsa na shugaban majalisar dattijai, wasu kuma na fadin cewa zargin fashin bankin Offa, dakatar da wasu yan majalisun dattijan da kuma kutse a cikin kasafin kudi za su ci gaba da ziyartar zukatansu.

KARANTA WANNAN: Ba sani ba sabo: EFCC ta kafa kwamitin binciken wasu gwamnoni guda 4 da zaran wa'adinsu ya kare 45 seconds ago

Yan Nigeria sun lissafa abubuwan da za su tuna da Saraki bayan karewar wa'adin wakilcinsa
Yan Nigeria sun lissafa abubuwan da za su tuna da Saraki bayan karewar wa'adin wakilcinsa
Asali: Depositphotos

Da me al'umma za su tuna da Saraki bayan karewar wa'adin wakilci da shugabancin majalisar dattijai?

Lisandro Silver, ta ce: "A wasu lokuta, yakan yi amfani da karfin ikonsa na shugabancin majalisar wajen kulle majalisar tarayya ta yadda zai samu damar tafiya yawo da Atiku, wannan kuwa abun kunya ne."

Inon Ekulide ya ce: "Majalisar dattijai ake magana ba wai shugaban majalisar ba. Shi daya ne a cikin miliyoyi. Duk wasu zarge zarge da ake yi akan sa shirmen banza ne, ku kyale Saraki ya sarara. Babu abunda Saraki ya rasa, amma jihar Kwara ta yi asarar komai musamman na rasa hazikin sanata."

A bangaren Liberato Nwogeh kuwa, "Mai karya doka, mai nuna kabilanci, adawa da dokar tsayawa takarar masu karancin shekaru, satar sandar girma, da kuma nuna adawa mai tsanani."

Nafiu Bolaji ya ce: "Za a tuna da Saraki da abubuwa masu yawa. A mulkinsa ne majalisar dattijai ta umurci hukumar kula da wutar lantarki ta kasa, NERC da ta gaggauta kawo karshen kudaden shan wuta da ake jibgawa 'yan Nigeria."

S. A Ibrahim ya bayyana cewa: "Za a tuna da shi saboda kayar da gwamnatin tarayya a kotun CCT da kuma aita kanta kotun, uwa uba kuma majalisa karkashinsa ta gudanar da ayyuka fiye da sauran majalisun da suka gabata."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel