Mutane su na so su san nawa ‘Yan Majalisa su ke kashewa a duk shekara

Mutane su na so su san nawa ‘Yan Majalisa su ke kashewa a duk shekara

Yayin da wa’adin shugabannin majalisar tarayya ta 9 yake gab da zuwa karshe, mun samu labari daga Jaridar Premium Times cewa an soma taso Bukola Saraki da kuma Rt. Hon. Yakubu Dogara a gaba.

Dalilin da ya sa aka hurowa shugabannin majalisar wuta shi ne domin ganin an daina boyewa jama’a harkar da ta shafi kasafin majalisa. Da-dama su na nema a rika bayyanawa Duniya abin da ‘yan majalisan kasar su ke kashewa.

Mutanen Najeriya sun dawo da batun nan na #OpenNASS da aka fara a 2015 lokacin da aka yi ta fafatukar ganin cewa majalisar tarayya ta fito fili ta bayyanawa kowa abin da ta ke batarwa a kowace shekara daga cikin kasafin kudi.

KU KARANTA: Ba za mu raba shugabancin Majalisa da 'Yan PDP ba – Inji APC

Mutane su na so su san nawa ‘Yan Majalisa su ke kashewa a duk shekara
Ana so Majalisa ta daina nuku-nuku game da kasafin kudin ta
Asali: Facebook

Yanzu haka an sake dawowa da wannan kuka ana rokon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara na majalisar wakilai da su daina boye-boye, su bayyana adadin Biliyoyin kudin da su ke warewa kan su.

A halin yanzu, Bukola Saraki da Yakubu Dogara su na shirin barin gadon mulki ne bayan da Yakubu Dogara ya koma jam’iyyar PDP maras rinjaye a majalisa yayin da shi kuma Bukola Saraki ya sha kasa a zaben bana a jihar sa.

Binciken BudgIT tayi ya nuna tsakanin 2003 zuwa 2018, abin da ake warewa ‘yan majalisar Najeriya ya tashi daga Biliyan 23 zuwa Naira Biliyan 139.5. Majalisar kasar ta na ma’aikata kusan 1000 ne da ke kashe wannan makudan kudi.

KU KARANTA: Sanatan Zamfara ya Shugaban Jam'iyyar Oshiomhole shawara

‘Yan majalisa a Najeriya su na kashe abin da ya zarce kasafin kudin jihohi 21 na kasar nan. Jaridar tace a 2017 ne kurum ‘Yan majalisar kasar su ka fadi adadin kudin da za su kashe inda aka ga ya zarce kasafin ma’aikatu 20 na gwamnati.

Mutane a kafafen yada labarai na zamani irin su Franklin Odukwu sun yi kira ga shugabannin majalisar da su fito da kason kudin su fili. Haka ma dai Adegbite Bolaji da Coker Adeniran sun yi irin wannan roko a shafin su na zamani na Tuwita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel