Naira Miliyan 54 sun fada hannun EFCC a filin jirgin Borno

Naira Miliyan 54 sun fada hannun EFCC a filin jirgin Borno

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa tayi nasarar kama wasu makudan miliyoyin kudi a babban filin jirgin saman nan na jihar Borno da ke cikin Garin Maiduguri.

EFCC ta cafke Naira miliyan 54 ne daga hannun wasu mutane 4 da kuma wasu kungiyoyi 2 masu zaman kan-su da ke aiki a jihar ta Borno kamar yadda bincike ya nuna. Sahara Reporters ta rahoto wannan a jiya Asabar 30 ga Watan Maris.

Hukumar ta EFCC ta bada sunayen wadanda ake zargi da mallakar wannan kudi da; Abdullahi Yarima, Francis Bako, Saraya Umaru, da kuma James Yadzugwa. Yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike a kan wannan kudi da aka samu.

Haka zalika, kungiyoyin da ake zargin da hannun su a cikin safarar wannan miliyoyi su ne: Kungiyar Mercy Corps da kuma Development Exchange Centre da ke aiki a jihar ta Arewa maso Yamma a dalilin rikicin kungiyar Boko Haram.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya gabatar da addu'ar ba Gwamna Ganduje sa'a

Naira Miliyan 54 sun fada hannun EFCC a filin jirgin Borno
Hukumar EFCC ta yi ram da Miliyoyin kudi a Maiduguri
Asali: Facebook

Jaridar tace EFCC ta gano cewa wannan kungiya ta Mercy Corps' tana da asusu daban-dabam har 15 dauke da lambar BVN mabanbanta yayin da ita kuma Development Exchange Centre ta ke da akalla akawun 40 dabam da juna.

Hukumar tace a Ranar 18 ga Maris dinnan ne ta gano wannan kudi inda ta soma bincike har ya kai aka kama Francis Bako da wata Baiwar Allah mai suna Saraya Umoru da ke aiki tare da kungiyar Development Exchange Centre.

A binciken da hukumar kasar tayi ta gano cewa an cire wannan kudi ne daga Sterling Bank bayan an shigo da kudin cikin asusun bankin daga Zenith Bank. Irin su Kungiyar Int’l FCStone Nigeria Ltd duk su na da hannu a wannan safara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel