Bauchi: Sanata Bala Mohammed ya karbi takardar shaidar cin zabe, ya ce zai tafi da kowa

Bauchi: Sanata Bala Mohammed ya karbi takardar shaidar cin zabe, ya ce zai tafi da kowa

- Zababben gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya sha alwashin aiwatar da ayyukan ci gaba da kuma farfado da jihar daga dogon suman da ta yi

- Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ke gabatar masa da takardar shaidar cin zabe

- Sanata Mohammed ya bayyana zabensa a matsayin babbar nasara ga al'ummar jihar Bauchi wadanda ya ce sun kawo shi ga kujerar bayan kada masu kuri'unsu

Zababben gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya sha alwashin aiwatar da ayyukan ci gaba da kuma farfado da jihar daga dogon suman da ta yi na tsawon shekaru hudu da suka gabata domin ganin jihar ta kai ga mataki na gaba.

Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ke gabatar masa da takardar shaidar cin zabe.

Ya karbi takardar ne a matsayinsa na zababben gwamnan jihar Bauchi karkashin jam'iyyar PDP.

Kwamishinan INEC da ke kula da ofishin hukumar na jihohin Bauchi, Gombe da Yobe, Baba Shettima Arfo shi ya raba takardun a yayin bukin da ya gudana a shelkwatar hukumar da ke Bauchi, a ranar Asabar.

KARANTA WANNAN: Zuwa mataki na gaba: Buhari ya fadi hanyar da zai bi wajen zabar mukarrabai

Bauchi: Sanata Bala Mohammed ya karbi takardar shaidar cin zabe, ya ce zai tafi da kowa
Bauchi: Sanata Bala Mohammed ya karbi takardar shaidar cin zabe, ya ce zai tafi da kowa
Asali: UGC

Mataimakinsa, Sanata Baba Tela da zababbun 'yan majalisun dokokin jihar guda 31 suma sun karbi takardun shaidar cin zabe daga hannun kwamishinan hukumar zaben na jihar, Ibrahim Abdullahi.

Zababbun 'yan majalisun dokokin jihar guda 31 sun fito ne daga jam'iyyun APC, PDP da NNPP.

Da ya ke jawabi bayan bukin mika takardun, Sanata Mohammed ya bayyana zabensa a matsayin babbar nasara ga al'ummar jihar Bauchi wadanda ya ce sun kawo shi ga kujerar bayan kada masu kuri'unku.

"A yau, ta tabbata cewa kokarin al'ummar jihar Bauchi da suka nuna a ranar 9 ga watan Maris bai tashi a banza ba. Ina matukar godiya ganin yadda jihar Bauchi ta amsa amo da murya daya kuma ina matukar godiya da samu zarafin amfana da wannan kokarin.

"Da wannan, na sha alwashin tafiya da kowa, yin adalci ga kowa da kuma yin shugabanci na-gari ta hanyar cika alkawuran da muka dauka yayin yakin zabenmu. Idan muka kama ragamar mulki, zamu tabbata mun bunkasa jihar Bauchi kuma ba zamu maimaita kuskuren gwamnatin da za ta shude ba," a cewar sa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel