Marafa ga Oshiomhole: Kada ka sauya daga shugaba zuwa makaryaci

Marafa ga Oshiomhole: Kada ka sauya daga shugaba zuwa makaryaci

Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan man fetur, Sanata Kabiru Garba Marafa (APC, Zamfara) ya bukaci Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole da ya ci gaba da kasance a matsayinsa na shugaba, sannan kada ya bari matsin lamba daga wasu barayin mutane ya sauya shi.

Da yake martani ga jawabin Oshiomhole a wani shirin Channels Tv, Marafa yace:

“Abun bakin ciki ne ganin mutum mai muhimmanci kamar Oshiomhole zai woffantar da sunansa a gaban idon duniya.

“Cif Oshiomhole yayi matukar kokari a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar, ya jagoranci jam’iyyar ta yadda ya ba kowa sha’awa, harma ga wadanda ke jam’iyyun adawa. Ya hada kai da al’umma, harma ya saba da wasu gwanonini da ke kokarin yin fin karfi a jihohinsu.”

Marafa ga Oshiomhole: Kada ka sauya daga shugaba zuwa makaryaci
Marafa ga Oshiomhole: Kada ka sauya daga shugaba zuwa makaryaci
Asali: Depositphotos

Marafa yayi mamaki kan dalilin da yasa babban mutum kamar Oshiomhole ke son kai kansa matsayi na makaryaci a wannan matsayi na rayuwarsa. Ya shawarci Oshiomhole da kada ya bari matsin lamba daga miyagun mutane maswu aikata zunubi, ya kais hi ga sauya halinsa na mutunci zuwa na mara mutunci.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC na shirin fara zawarcin yan PDP

“Abunda Oshiomhole ya fadi ba komai bane face karya da ba zai taba tasiri ba.

“Hujjoji da takardu sun nuna cewa APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba a jihar Zamfara, saboda taurin kai irin na gwamnan jihar wanda yayi barazana a bainar jamaá cewa zai aika Oshiomhole kushewa idan har ya yi wasa dashi."

Ya bukaci Oshiomhole da yayi koyi da tsarin mulki irin na Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ke tsaye akan gaskiya, koda kuwa hakan zai bata wa jam’iyyarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel