Jam’iyyar APC na shirin fara zawarcin yan PDP

Jam’iyyar APC na shirin fara zawarcin yan PDP

Wani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Farouk Adamu Aliyu ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta koyi darasi akan yadda aka gudanar da zabubbukan kasar na wannan shekarar.

A wata hira da ya yi da shafin BBC ya bayyana cewa rabuwar kan 'yan takara na daya daga cikin abubuwan da suka kawo ma jam'iyyar cikas, har zama ta fuskanci kalubale a wasu jihohi wanda hakan ya yi tasiri wajen rasa wasu kujerun gwamnoni da ma na 'yan majalisa.

Ya yi misali da jihar Ogun inda ya bayyana cewa gwamnan ya yi ungulu da kan zabo inda gwamnan jihar dan APC ne amma ya jagoranci wata jam'iyya domin ganin cewa an kada jam'iyyar APC a zaben gwamna.

Jam’iyyar APC na shirin fara zawarcin yan PDP
Jam’iyyar APC na shirin fara zawarcin yan PDP
Asali: Twitter

Ya yi kira ga jam'iyyar APC mai mulki a kasar kan cewa a shekarar 2023 ta tabbatar an yi zaben fitar da gwani na jam'iyyar sahihi kuma ingantacce a duk fadin kasar.

Farouk wanda ya kasance tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, ya ja hankalin Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan cewa alúmman kasar sun nuna masa soyayya a duk jam'iyyar da ya shiga, saboda haka ya zama wajibi ya tabbatar da cewa APC ta dore.

KU KARANTA KUMA: Sarki Sanusi II ya shirya addu'a ta musamman don taya Ganduje murna

Daga karshe Farouk ya kara bayyana cewa za su ci gaba da zawarcin wadanda suka sauya sheka daga jam'iyyar APC don ganin cewa an dawo da su saboda tafiya tare.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai zabi mukarraban gwamnatinsa a wannan karon bisa la'akari da cancanta da kuma dai-daito.

Ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin shuwagabannin addinai a fadar shugaban kasa Abuja, inda ya basu tabbacin cewa gwamnatinsa za ta tabbata ta bar kyakkyawan tarihi a Nigeria fiye da lokacin da ya same ta a 2015.

Ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen magance muhimman lamuran da ke ciwa kasar tuwo a kwarya da suka shafi tsaro, tattalin arziki da cin hanci da rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel