Zuwa mataki na gaba: Buhari ya fadi hanyar da zai bi wajen zabar mukarrabai

Zuwa mataki na gaba: Buhari ya fadi hanyar da zai bi wajen zabar mukarrabai

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai zabi mukarraban gwamnatinsa a wannan karon bisa la'akari da cancanta da kuma dai-daito

- Ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da magance manyan matsalolin kasar kamar tsaro, tattalin arziki da cin hanci da rashawa

- Buhari ya sha alwashin ci gaba da goyon bayan dukkanin shirye shiryen da NIREC ke shiryawa domin wanzar da zaman lafiya da hadin kan jama'a baki daya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai zabi mukarraban gwamnatinsa a wannan karon bisa la'akari da cancanta da kuma dai-daito. Ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin shuwagabannin addinai a fadar shugaban kasa Abuja, inda ya basu tabbacin cewa gwamnatinsa za ta tabbata ta bar kyakkyawan tarihi a Nigeria fiye da lokacin da ya same ta a 2015.

Buhari a lokuta daban daban, ya karbi bakuncin kungiyar kiristoci ta Nigeria CAN bisa jagorancin Dr. Samson Ayokunle, da kuma tawagar limamai da manyan malaman addinin Musulunci bisa jagorancin Farfesa Shehu Galadanci.

Ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen magance muhimman lamuran da ke ciwa kasar tuwo a kwarya da suka shafi tsaro, tattalin arziki da cin hanci da rashawa.

KARANTA WANNAN: Maganar gaskiya: Ba mu da kudurin hargitsa zaben Rivers, karya ake mana - DSS

Zuwa mataki na gaba: Buhari ya fadi hanyar da zai bi wajen zabar mukarrabai
Zuwa mataki na gaba: Buhari ya fadi hanyar da zai bi wajen zabar mukarrabai
Asali: Twitter

"Zamu ci gaba da bin matakai na wanzar da zaman lafiya a tsakanin 'yan Nigeria ba tare da yin duba da banbancin addini ba. A bangaren rabon mukamai kuwa, zamu mayar da hankali wajen duba cancanta da kuma dai-daito ta yadda kowanne bangare na Nigeria zai shaida da wannan mulki namu.

"Zamu ci gaba da aiki tukuru wajen ganin mun yaki ta'addanci da yan ta'adda, da kuma ci gaba da yunkurin ganin mun kwato sauran wadanda aka yi garkuwa da su," a cewar sa.

Da ya ke bayyana muhimmiyar rawar da addinai ke takawa wajen ganin gwamnati ta samu nasara a shekaru hudun da suka gabata, Buhari ya sha alwashin ci gaba da goyon bayan dukkanin shirye shiryen da majalisar addinai ta kasa NIREC ke shiryawa domin wanzar da zaman lafiya, jin kai da hadin kan jama'a baki daya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel