Sarki Sanusi II ya shirya addu'a ta musamman don taya Ganduje murna

Sarki Sanusi II ya shirya addu'a ta musamman don taya Ganduje murna

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shirya taron addu'a na musamman a ranar Asabar domin taya Gwamna Abdullahi Ganduje murnar lashe zabe da rokon Allah ya yi masa jagoranci a mulkinsa karo na biyu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan magoya bayan Ganduje sun cire hotunnan Sarki Sanusi da ke ciki da wajen dakin taron nadin sarauta na Kano da ke gidan gwamnati sakamakon zargin sarkin da marawa dan takarar jam'iyyar PDP baya.

Sai dai kwanaki kadan bayan cire hotunan, Gwamna Ganduje ya bayar da umurnin a mayar da hotunan inda ya ce duk da cewa Sarkin yana shiga harkokin siyasa, babu wani shirin tsige shi a yanzu.

Sarki Sanusi II ya shirya addu'a ta musamman don taya Ganduje murna
Sarki Sanusi II ya shirya addu'a ta musamman don taya Ganduje murna
Asali: Twitter

Amma kuma sai gashi Sarkin ya shirya taron addu'a na musamman a babban masallacin Kano domin taya Ganduje murnar lashe zabe da fatan Allah ya yi masa jagora a mulkinsa karo na biyu kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar ya sanar.

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa

"Wadanda suka hallarci taron sun hada da hakimai, limamai na Kano da masu nazarin ilimin addinin musulunci a yayin da shi kuma Ganduje ya hallarci taron tare da wasu 'yan fadarsa, da masu bashi shawara na musaman da sauransu.

"Sarki Sanusi ya dauki lokaci mai tsawo yana bayyani a kan muhimmancin yafiya da afuwa a kan duk wani harka na gwamnati da alaka tsakanin al'umma inda ya ce 'yan kora ne ke janyo rashin jituwa tsakanin al'umma. Ya ce dole mu rika addu'a Allah ya kare mu daga sharrinsu."

Sarki Sanusi ya cigaba da cewa, "Ba laifi bane mutum ya fadi ra'ayinsa a kan abubuwa da ke faruwa a tsakanin al'umma. Amma abinda ke da muhimmanci shine bayan zabe, al'umma su hada kansu wuri guda su goyi bayan wanda ya yi nasara."

"Ya zama dole mu hada hannu wuri guda mu gina jihar Kano. Ya zama dole muyi aiki tukuru kuma muyi addu'a domin samun cigaba a jihar mu da kasar mu baki daya.

"Muna fata Allah ya kiyaye mu daga sharin munafikai daga dukkan bangarori. Za mu cigaba da addu'a samun zaman lafiya a jihar mu. Ya kamata al'umma su fahimci abinda ya fi muhimmanci shine suyi addua'a Allah ya taimaki shugabanin mu. Ya kuma basu masu shawara na gari."

Ya kuma shawarci gwamna Ganduje ya rika bincike a kan duk wani labari a aka kawo masa domin a wasu lokutan mutane na iya kirkirar labari domin su haifar da rashin jituwa tsakanin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel