Ta faru ta kare: Nnamdi Kanu ya mayarwa da kotu martani, ya ce shi ba dan Najeriya ba ne

Ta faru ta kare: Nnamdi Kanu ya mayarwa da kotu martani, ya ce shi ba dan Najeriya ba ne

- A satin nan da ya gabata kotu ta ba da umarnin a kamo shugaban 'yan kungiyar Biafra, Nnamdi Kanu

- To sai gashi shi ma yau shugaban su ya maryawa da kotun martani, akan cewa shi ba dan Najeriya ba ne saboda haka dokar Najeriya ba za ta hau kan shi ba

A yau Asabar dinnan ne, shugaban kungiyar ma su kokarin kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ba wa mutane da yawa mamaki, a lokacin da ya bayyana cewa shi ba dan Najeriya ba ne, kuma ba shi da wata alaka da Najeriya.

A lokacin da yake bayanin, a gidan Radiyon Biafra, Kanu ya ce zai kalubalanci kotun da ta ba da damar kamo shi a birnin Landan.

Ta faru ta kare: Nnamdi Kanu ya mayarwa da kotu martani, ya ce shi ba dan Najeriya ba ne
Ta faru ta kare: Nnamdi Kanu ya mayarwa da kotu martani, ya ce shi ba dan Najeriya ba ne
Asali: Facebook

Idan baku manta ba, majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton cewa wata Kotun Koli da ke Abuja ta bayar da damar kamo Kanu a duk inda yake, saboda ya ki bayyana a gabanta.

KU KARANTA: Kotu ta sa a kamo Nnamdi Kanu a duk inda ya ke

A lokacin da ya ke magana da manema labarai, Kanu ya ce "duk wani yunkuri da gwamnati ta yi akan kamo shi a shirye ya ke, kuma zamu kalubalanci kowacce kotu a birnin Landan shi da lauyoyinsa.

"Sannan kuma ni ba dan Najeriya ba ne, saboda haka shari'arku ba za ta yi aiki a kaina ba, kuma duk wanda ya ke so ya ji dalilina na kin komawa kotu to ya fara tambayar sojojin da su ka je gidana mai su ka je yi?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel