'Yan bindiga sun bude wuta a wurin taron bikin kamun kifi a Kogi, mutane 5 sun jikkata

'Yan bindiga sun bude wuta a wurin taron bikin kamun kifi a Kogi, mutane 5 sun jikkata

A yau Asabar 30 ga watan Maris ne wasu 'yan bindiga suka tarwatsa taron bikin kamun kifi na Dankwo da ake gudanarwa duk shekara-shekara a garin Lokoja bayan sun bude wuta ga mahallarta taron.

Kamfanin dillancin labarai, NAN ta ruwaito cewa an fara bikin da misalin sa'a guda ne lokacin da 'yan bindigan suka kawo farmaki inda ake bikin a rafin Kabawa cikin kwale-kwale mai inji.

'Yan bindigan da suka taho su uku a cikin kwale-kwale mai inji sunyi ruwan harsashi a cikin taron wanda haka ya sa al'umma suka fara tserewa sai dai sun harbi mutane biyar.

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa

'Yan bindiga sun bude wuta a wurin taron bikin kamun kifi a Kogi, mutane 5 sun jikkata
'Yan bindiga sun bude wuta a wurin taron bikin kamun kifi a Kogi, mutane 5 sun jikkata
Asali: Twitter

An sanar da jami'an 'yan sanda nan take sai dai kafin su iso wurin 'yan bindigan sun tsere a cikin kwale-kwalen da suka taho.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kogi, DSP William Aya ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce abin bakin ciki ne.

A cewarsa, dukkan mutane biyar da suka jikkata suna nan da ransu suna karbar magani a cibiyar lafiya na gwamnatin tarayya da ke Lokoja.

Ya ce babu wanda ya mutu sakamakon harin kuma tuni an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a cikin kai harin.

Aya ya ce an fara cikaken bincike a kan harin kuma za a hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin aikata wannan mummunan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel