Yiwa jam'iyya zagon kasa: Fadar shugaban kasa ta juya wa Okorocha baya

Yiwa jam'iyya zagon kasa: Fadar shugaban kasa ta juya wa Okorocha baya

- An samo rahotannin cewa fadar shugaban kasa da jam'iyyar APC suna shirin ladabtar da Gwamna Rochas Okorocha

- Gwamnan na jihar Imo ya dade suna sa-in-sa da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC karkashin jagorancin Adams Oshiomhole

- A baya an dakatar da Okorocha daga jam'iyyar saboda yiwa jam'iyya zagon kasa sannan yanzu ya shiga wata matsalar saboda INEC ta ki bashi takardan shaidan cin zabe

Rahotannin daga wata majiya na cikin gida na nuna cewa jam'iyyar All Progressive Congress, APC da fadar shugaban kasa sun kammala shirin ladabatar da Gwamnan Imo mai barin gado, Rochas Okorocha a yanzu da ya ke fuskantar sakamakon yiwa jam'iyyarsa zagon kasa yayin zaben 2019.

Legit.ng ta ruwaito cewa Okorocha da jam'iyyar ta APC karkashin jagorancin Adams Oshiomhole sun dade ba su ga maciji tun bayan dakatar da gwamnan da jam'iyyar tayi sakamakon zargin da ake masa na yiwa jam'iyya zagon kasa.

DUBA WANNAN: INEC ta tsayar da ranar bawa Ganduje da 'yan majalisun jiha takardun shaidan cin zabe

Yiwa jam'iyya zagon kasa: Fadar shugaban kasa ta juya wa Okorocha baya
Yiwa jam'iyya zagon kasa: Fadar shugaban kasa ta juya wa Okorocha baya
Asali: UGC

Gwamnan na jihar Imo ya janyo wa kansa fushin APC ne bayan ya yi watsi da dan takarar gwamna na APC, Hopoe Uzodinma ya koma yana goyon bayan surukinsa da ke takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Action Alliance (AA) wanda hakan ya janyo APC ta sha kaye a zaben.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta ki bashi takardan shaidan cin zabe bayan baturen zabe na jihar ya ce an tilasta masa fadin cewa Okorocha ne ya lashe zaben Sanata na yankin Imo ta Yamma.

Daga baya da gwamnan ya lura jam'iyyar APC ta juya masa baya game da rashin bashi takardan shedan cin zabe da INEC tayi, ya canja salo ya fara neman sulhu.

A cewar Vanguard, gwamnan ya fara neman kamun kafa daga wasu jiga-jigan APC da fadar shugaban kasa amma babu wanda ya kula shi.

Wata majiyar ta ce: "Gwaman ya bawa wasu jiga-jigan jam'iyyar tabbacin cewa surukinsa ne zai lashe zabe sannan ya dawo jam'iyyar APC daga baya.

"Sun amince da hakan kuma suka ki bamu hadin kai da muke bukata kuma gashi abinda hakan ya haifar, mun rasa jiya daya tilo da muke dashi a Kudu maso gabas.

"Ya munafinci kowa a fadar shugaban kasa inda ya ce zai iya lashe zabe kuma surukinsa zai koma jam'iyyar APC bayan ya lashe zabe. Hakan yasa wasu suka mayar da hankali a kansa yayin da Hope Uzodinma ba samu irin tallafin da ya ke bukata ba.

"Yanzu fadar shugaban kasa tana fushi da shi saboda ya gaza cika alkawarin da ya dauka, ya bari PDP ta kwace jiya daya da muke dashi a Kudu maso gabas.

"Yanzu jiga-jigan jam'iyyar da fadar shugaban kasa duk sun juya masa baya, babu wanda ke son ganinsa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel