Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa suyi

Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa suyi

Jogaran jam'iyyar APC na kasa, Ahmed Bola Tinubu ya ce dole sabbin zababun 'yan majalisa suyi biyaya ga dokokin jam'iyya ko kuma su fita daga jam'iyyar.

Mr Tinubu ya ce dole ayi biyaya ga shugabanin jam'iyya wurin zaben shugaban majalisar dattawa na majalisa karo na 9.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a a Legas bayan wata addu'a na musamman da malaman addinin musulunci da kirista suka shirya domin murnar cikarsa shekaru 67 a duniya.

DUBA WANNAN: INEC ta tsayar da ranar bawa Ganduje da 'yan majalisun jiha takardun shaidan cin zabe

Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa suyi
Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa suyi
Asali: UGC

"Ladabi ga jam'iyya shine mafita, dole mu kasance masu ladabi a jam'iyyar mu. Munyi sakaci a 2015. Mu bawa munafukai dama sun shiga jam'iyyar mu kuma hakan ya janyo koma baya wurin cigaban kasa.

"Kun ga sakamakon hakan saboda haka ba zamu sake barin hakan ya faru ba. Za mu girmama jam'iyyar mu kuma za muyi amfani da tsumagiyya.

"Zabin da ya rage shine ko mutum ya yi tafiya tare da mu ko ya fice daga jam'iyyar. Kana da zabin kayi abinda ka ke so amma ba zamu baka dama kayi amfani da jam'iyyar mu ba wurin hada kai da wata jam'iyyar adawa.

"Ba zamu amince da hakan ba wannan karon, ko kai waye. Haka dama aka kafa jam'iyyar. Mene yasa ba ka son yin biyaya ga dokokin jam'iyyar?

"Zamu bawa ko wane yankin hakkin ta," inji Tinubu.

Shugabanin jam'iyyar APC sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Ahmed Lawan domin zama shugaban majalisar dattawa sannan shi kuma Femi Gbajabiamila ake son ya zama Kakakin majalisar dokoki na tarayya.

Sai dai wasu 'yan majalisun APC sun soki hakan, cikinsu har da Sanata Ali Ndume da ke takarar shugabancin majalisar inda ya ce ba zai ajiye takararsa ba tunda sanatocin APC da dama suna tare da shi.

Sanata Danjuma Goje daga jihar Gombe shima yana sahun masu takarar shugabancin majalisar dattawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel