INEC yakar mu tayi a zaben 2019 - Oshiomhole

INEC yakar mu tayi a zaben 2019 - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa Adams Oshiomhole ya yi zargin cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC ta tauye wa jam'iyyarsa hakokinta a babban zaben 2019 da aka kammala.

Oshiomhole ya yi wannan zargin ne a wata hira da akayi da shi a gidan talabijin na Channels a wani shiri mai taken 'Hard Copy' a ranar Juma'a.

"Ban gamsu da yadda INEC ta gudanar da zabe ba. Rashin adalci da INEC ta yiwa APC abu ne da ya fito fili karara," inji shi.

"INEC ba ta yi mana adalci ba a kan batun zaben cikin gida da muka yi, INEC ta nuna wariya a kan yadda ta zabi wuraren da tayi amfani da na'urar tantance katin zabe da kuma rashin amfani da shi a wuraren da ta ga dama."

DUBA WANNAN: INEC ta tsayar da ranar bawa Ganduje da 'yan majalisun jiha takardun shaidan cin zabe

INEC yakar mu tayi a zaben 2019 - Oshiomhole
INEC yakar mu tayi a zaben 2019 - Oshiomhole
Asali: Depositphotos

Tsohon shugban kungiyar kwadagon ya yi ikirarin cewa rashin amfani da card reader a wasu jihohi ne dalilin da yasa APC ta sha kaye.

Jam'iyyar APC ta rasa kujerun gwamna a jihohi hudu da ta ke mulki a halin yanzu wato jihohin Imo, Ogun, Adamawa da Bauchi, tayi nasara a jihohi biyu da jam'iyyun adawa ke mulki (Kwara da Gombe).

Mr Oshiomhole ya ce ba zai taba kare rashin adalcin da INEC tayi ba a wurin gudanar da zaben 2019.

Shima dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya koka kan rashin amfani da card reader da INEC ba tayi ba a dukkan wuraren zabe.

Atiku Abubakar yana kallubalantar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a zaben na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel