Tinubu ya bayyana kura-kuran da jam'iyyar APC ta aikata a shekarar 2015

Tinubu ya bayyana kura-kuran da jam'iyyar APC ta aikata a shekarar 2015

- Tinubu ya shawarci duk wani dan jam'iyyar APC da ba zai bi dokar jam'iyya ba da ya koma wata jam'iyyar

- Sannan ya bayyana cewa jam'iyyar APC ba za ta sa ke aikata kuskuren da ta yi a baya ba

A wata tattaunawa da aka yi da tsohon gwamnan jihar Lagos, kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce dole ne jam'iyyar ta yi iya bakin kokarinta wurin ganin ba ta maimaita kuskuren da ta yi a baya ba, a shekarar 2015.

Tinubu ya ce a wancan lokacin jam'iyyar ta yi sakaci da yawa wanda har ta baiwa bara-gurbi damar shigowa jam'iyyar. Ya yi maganar ne a gidansa da ke jihar Lagos, a lokacin da ake yi ma sa addu'ar cika shekaru 67 a duniya.

Tinubu ya bayyana kura-kuran da jam'iyyar APC ta aikata a shekarar 2015
Tinubu ya bayyana kura-kuran da jam'iyyar APC ta aikata a shekarar 2015
Asali: UGC

A lokacin da yake magana da manema labaran, Tinubu ya ce duk wani dan jam'iyyar APC da ya san ba zai bi dokar da jam'iyya ta sa ka ba, ya na da damar da zai iya barin jam'iyyar.

KU KARANTA: An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi

Idan ba a manta ba majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku labarin yadda jam'iyyar APC ta fitar da Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda zai shugabanci majalisar dattawa. Sannan kuma akwai kananan maganganu da su ke nu ni da cewa 'yan majalisu su na zargin shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole akan yanke hukunci ba tare da neman shawarar 'yan jam'iyya ba.

Sanata Ali Ndume na jihar Borno shi ma ya bayyana kudurin sa na neman kujerar shugaban majalisar dattawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel