Rashin fitar da shugaban majalisar dattijai zai bar baya da kura - PLAN

Rashin fitar da shugaban majalisar dattijai zai bar baya da kura - PLAN

- An gargadi jam'iyyar APC ta fitar da shugaban majalisar dattawa, kafin a fara samun rabuwar kai a majalisa

- Wata kungiya mai hulda da majalisun dokoki ita ce ta yi wannan gargadi

Wata kungiya mai hulda da majalisun dokokin Najeriya ta gargadi jam'iyyar APC akan ta maida hankali wurin fitar da wanda zai jagoranci majalisar dattawa, sannan kungiyar ta ce rashin yin hakan zai saka 'yan majalisa su yi wa jam'iyyar tawaye.

Shugaban kungiyar Lord Charles Ibiang, ya ce duk da cewa adalci ne a fitar da shugaban majalisar dattawa daga yankin arewa maso gabas, amma hakan kar ya sa jam'iyya ta dinga bata lokaci wurin fitar da shugaban majalisar.

Rashin fitarda shugaban majalisar dattijai zai bar baya da kura - PLAN
Rashin fitarda shugaban majalisar dattijai zai bar baya da kura - PLAN
Asali: Facebook

A cewarshi, kamata yayi ace jam'iyyar APC ta tina abinda ya faru a baya, lokacin da ta ke kokarin fitar da shugabannin majalisa, hakan ya kawo tawaye a majalisar dattijai, da ma ta wakilai gaba daya, bayan haka kuma akwai kwararrun Sanatoci a yankin arewa maso gabas, wanda bai kamata ace an tsaya ana bata lokaci wurin zabar su ba.

KU KARANTA: An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi

Saboda haka ya kamata Sanatoci su ta shi tsaye, domin ganin an gabatar da wanda zai jagoranci majalisarsu, ko dan saboda 'yan Najeriya da su ka zabe su, kuma ya kamata ku zabi shugaba wanda ya san zafi da darajar mutane, shugaba wanda zai yi aiki saboda talakawa, sannan shugaba wanda zai yi kokari wurin ganin kan al'ummar kasar nan ya hadu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel