Maganar gaskiya: Ba mu da kudurin hargitsa zaben Rivers, karya ake mana - DSS

Maganar gaskiya: Ba mu da kudurin hargitsa zaben Rivers, karya ake mana - DSS

- Hukumar tsaro ta DSS ta karyata zargin cewar an bata umurnin amfani da karfin ikonta domin ganin an ki kammala zaben iihar Rivers

- Mr Peter Afunanya, jami'in hulda da jama'a na hukumar tsaro ta DSS ya bayyana matsayar hukumar tsaron a ranar Juma'a a Abuja

- INEC ta sanya ranar 2 ga watan Afrelu da 5 ga wata domin fadin sakamakon zaben da aka rigaya aka fara hadawa, yayin da karashen zabukan zai zo a ranar 15 ga watan

Hukumar tsaro ta cikin gida DSS ta karyata zargin da ake yi mata na cewar an bata umurnin amfani da karfin ikonta domin ganin an ki kammala zaben iihar Rivers.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da aka kad'a a ranar 23 ga watan Maris a jihar Rivers.

Hukumar ta sanya ranar 2 ga watan Afrelu da 5 ga wata domin tattarawa tare da fadin sakamakon zaben da aka rigaya aka fara hadawa, yayin da za ta gudanar da karashen zabukan a ranar 15 ga watan Afrelu a wasu sassa na jihar.

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: Jigawa ta tsaida ranar 29 ga watan Yuni domin gudanar da zaben kansiloli

Maganar gaskiya: Ba mu da kudurin hargitsa zaben Rivers, karya ake mana - DSS
Maganar gaskiya: Ba mu da kudurin hargitsa zaben Rivers, karya ake mana - DSS
Asali: UGC

Mr Peter Afunanya, jami'in hulda da jama'a na hukumar tsaro ta DSS ya bayyana matsayar hukumar tsaron a ranar Juma'a a Abuja.

Ya ce babu wani umurni da hukumar ta samu na hargitsa tsarin zaben jihar kamar yadda wasu ke zargi.

"A matsayinmu na kwararru, hukumarmu za ta ci gaba da bin tsari na gaskiya da adalci," a cewar sa.

Afunanya ya ce wannan kuwa na daga cikin matsayar shugaban kasa Muhammadu Buhari na haramtawa jami'an tsaro tsoma hannu ko sa baki a harkokin siyasarkasar.

Kakakin hukumar ya kuma ce hukumar DSS za ta hada hannu da sauran hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki dokin tabbatar da cewa an baiwa kowanne dan takara kyakkyawan yanayi na gudanar da zaben.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel