Ganduje ya rabawa 'yan bautar kasa naira dubu dari - dari

Ganduje ya rabawa 'yan bautar kasa naira dubu dari - dari

- Gwamna Ganduje ya yi wa wadansu 'yan bautar kasa abin a zo a yaba

- Gwamnan ya raba musu naira dubu dari-dari, sannan ya yi musu alkawarin ba su kulawa ta musamman, ya yi musu alkawarin ba su alawus kowane wata

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bawa 'yan bautar kasa guda 6 da 'yan fashi su ka kaiwa hari, N600,000.

Gwamnan wanda ya bada kyautar a ranar juma'a 29 ga watan Maris, ya ce ya ba da kudin ne saboda ya kwantarwa da wadanda abin ya shafa hankali. Sannan Gandujen ya roki 'yan bautar kasar da su zamanto mutane na gari, wadanda al'ummar baya da kasa zata yi alfahari da su.

Ganduje ya rabawa 'yan bautar kasa dubu dari - dari
Ganduje ya rabawa 'yan bautar kasa dubu dari - dari
Asali: Depositphotos

Sannan ya yiwa 'yan bautar kasar alkawarin ba su tsaro yadda ya kamata a fadin jihar Kano, sannan ya yi musu alkawarin zai cigaba da basu alawus na N5,000 da ya saba basu duk karshen wata.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga wani taron gaggawa da 'yan kungiyar CAN

Sannan ya kara da cewa, ma'aikatan fannin lafiya, za a ba su alawus fiye da na kowa.

Ba dadewa, mu ka samu rahoton cewa 'yan fashi sun kaiwa wasu masu bautar kasa su 6 hari, akan hanyar Gwarzo zuwa Karaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel