Da zafinsa: Jigawa ta tsaida ranar 29 ga watan Yuni domin gudanar da zaben kansiloli

Da zafinsa: Jigawa ta tsaida ranar 29 ga watan Yuni domin gudanar da zaben kansiloli

- Hukumar zabe ta jihar Jigawa (JISIEC) ta sanya ranar 29 ga watan Yuni ta zamo ranar da zata gudanar da zaben kansilolin jihar

- Hukumar dai ta ce tuni ta kammala dukkanin shirye shirye na gudanar da zaben

- Ta tsaida ranar 22 ga watan Afrelu domin fara sayar da fom na tsayawa takara, yayin da za a fara tantance 'yan gakara a ranar 26 ga watan Mayu

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Jigawa (JISIEC) ta sanya ranar 29 ga watan Yuni ta zamo ranar da zata gudanar da zaben kansilolin jihar a wannan shekarar.

Shugaban hukumar, Mohammed Sani Ahmad, ya bayyana hakan a ranar Juma'a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Dutse, yana mai cewa tuni hukumar ta kammala dukkanin shirye shirye na gudanar da zaben.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Mohammed Dantani, dan majalisar tarayya ya rasu a Abuja

Ya kara da cewa tuni hukumar ta fitar da jaddawalin ayyukanta gabanin zuwan ranar zaben, yana mai karawa da cewa a ranar 22 ga watan Afrelu ne za a fara sayar da fom na tsayawa takara, yayin da za a fara tantance 'yan gakara daga jam'iyyu daban daban a ranar 26 ga watan Mayu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel