Wani Bam din da Boko Haram suka birne ya tarwatse da sojojin Najeriya 13

Wani Bam din da Boko Haram suka birne ya tarwatse da sojojin Najeriya 13

A kalla sojoji 13 ne suka rasu kuma wasu da dama suka jikkata a ranar Litini a jihar Borno yayin da motar da suke ciki ta bi ta kan wani bam din da mayakan Boko Haram suke birne a kasa kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Sojojin suna tafiya ne a kan titin Gwoza zuwa Yamteke da ke karamar hukumar Gwoza a lokacin da babban motar sojojin ta bi ta kan bam din da 'yan ta'addan suka birne kuma ta tarwatsa motar.

Majiyar Legit.ng ta gano daga majiyar hukumomin tsaro cewa sojoji takwas sun mutu a nan take yayin da wasu uku suka sake mutuwa daga baya sannan wasu da damu sun jikkata.

DUBA WANNAN: Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa

Wani Bam din da Boko Haram suka birne ya tarwatse da sojojin Najeriya 13
Wani Bam din da Boko Haram suka birne ya tarwatse da sojojin Najeriya 13
Asali: Twitter

"Bam din karkashin kasa ya lalata babban motar sojoji kirar Mitsubishi; abin babu kyan gani kuma sojoji sun jikkata sosai," inji majiyar jami'an tsaron.

Sahara Reporters ta ce ta ga hotunan gawarwakin da suka tarwatse a matsayin shaidan afkuwar harin amma ba za a iya wallafa su ba saboda munin harin.

Kawo yanzu, rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai ba a kan afkuwar lamarin.

A kwana-kwanan nan dai mayakan kungiyar na Boko Haram sun tsananta kai hare-hare a kudancin jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel