INEC ta tsayar da ranar bawa Ganduje da 'yan majalisun jiha takardun shaidan cin zabe

INEC ta tsayar da ranar bawa Ganduje da 'yan majalisun jiha takardun shaidan cin zabe

Shugaban wayar da kan masu zabe na INEC reshen jihar Kano, Mallam Muhammad Garba Lawal ya ce za a bawa zababen gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna da 'yan majalisun dokokin 40 takardan shaidan lashe zabe a ranar Laraba na mako mai zuwa.

Shugaban sashin wayar da kan masu zabe da watsa labarai na INEC, Garba Lawal ne ya bayyana hakan yayin zantawar da ya yi da manema labarai a ranar Juma'a 29 ga watan Maris.

Garba ya ce ana sa ran kwamishinan INEC na kasa mai kula da jihohin Kano, Jigawa da Katsina, Injiya Abubakar Nahuche ne zai gabatar da takardun shaidan lashe zaben ga zababun shugabannin.

DUBA WANNAN: Zababun 'yan majalisan APC 16 a Sokoto sun ki zuwa karbar takardan shaidan cin zabe

Ganduje da sauran zabaun 'yan majalisun dokokin jihar Kano 40 za su karbi takardun shaidan lashe zabe a ranar Laraba
Ganduje da sauran zabaun 'yan majalisun dokokin jihar Kano 40 za su karbi takardun shaidan lashe zabe a ranar Laraba
Asali: Twitter

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe kujeru majalisar dokokin jihar 27 cikin 40 yayin da jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta lashe kujeru 13.

Gwamnan jihar mai ci yanzu kuma zababen gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ci galaba a kan abokin fafatawarsa na jam'iyyar PDP Abba Kabiru Yusuf da ratar kuri'u 8,982.

Baturen zabe na jihar Farfesa Bello B Shehu ya sanar da cewa Ganduje ya lashe zaben ne bayan an gudanar da zaben rabar gardama a jihar.

A jawabinsa da ya yi na samun nasara, Dr. Abdulllahi Umar Ganduje ya yi alkawarin cigaba da ayyukan da ya fara kuma ya ce zai yiwa kowa adalci a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel