Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa

Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi sallar Juma'a ne a masallacin fadar shugaban kasa a maimakon babban masallacin kasa na Abuja saboda kaucewa cinkoson da fitarsa ke janyo wa al'umma.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya ce shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya da tawagar limamai da manyan malaman addinin musulunci daga jihohi Najeriya suka yi masa yayin da suka kai masa ziyara a ranar Juma'a.

Tawagar limaman karkashin jagorancin Farfesa Shehu Ahmad Galadanci sun kai ziyara gidan gwamnati ne domin su yiwa shugaban kasar murna nasarar da ya yi a zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu.

DUBA WANNAN: Shugabancin majalisa: Buhari, gwamnoni da shugabannin APC sun lallashi Goje

Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa
Buhari ya fadi dalilinsa na yin sallar Juma'a a masallacin fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya ce: "A kan batun bukatar da kuka gabatar na nema in rinka zuwa sallar Juma'a a masallacin kasa, Ina rokon ku da ku fahimta cewa na fara yin sallar Juma'a ne a masallacin fadar shugaban kasa saboda in rage wahalhalun al'umma ke shiga idan na fita.

"Kamar yadda kuka sani, duk lokacin da shugaban kasa zai fita dole sai an takaita zirga-zirga a wasu wurare tare da kafa shinge a hanyoyi wanda hakan na iya janyo matsi ga masallata da sauran al'umma."

Shugaba Buhari ya gode wa malaman bisa addu'o'i da goyon bayan da suke bawa gwamnatinsa inda ya tabbatar musu ba zai yi kasa a gwiwa ba wurin magance kallubalen tsaro da kasar ke fama da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel