Ya kamata gwamnatin tarayya ta wanke ni a idon duniya - Onnoghen

Ya kamata gwamnatin tarayya ta wanke ni a idon duniya - Onnoghen

Bayan kotu ta kori tuhumar da ta ke yi mishi, tsohon alkalin ya bukaci gwamnatin tarayya ta wanke shi a idon duniya, a bisa dalilin da ya bayar na cewa gwamnati ba ta da wata shaida kwakkwara da za ta tabbatar da laifin da ta ke zargin shi da shi

Tsohon alkalin alkalai wanda gwamnatin tarayya ta dakatar, ya bukaci gwamnatin tarayyyar da ta wankeshi, akan tuhumarshi da ta ke na rashin bayyana kadarorinshi.

Ya kamata gwamnatin tarayya ta wanke ni a idon 'yan Najeriya - Onnoghen
Ya kamata gwamnatin tarayya ta wanke ni a idon 'yan Najeriya - Onnoghen
Asali: Twitter

Gwamnatin tarayya karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari ta dakatar da alkalin alkalan a ranar 25 ga watan Janairu, sai dai kuma shi alkalin ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta ba shi hakuri, tunda har yanzu gwamnatin tarayyar ba ta da wata hujja da take nu na cewa yana da laifi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya shiga wani taron gaggawa da 'yan kungiyar CAN

A cewarshi, "babu wata shaida da ta nu na cewar ina da laifi." Sannan kuma alkalin ya bukaci Mista Danladi Umar da kuma wasu mutane uku da su ke sauraron karar ta shi akan su kori karar ta shi sannan kuma a sauke duk wani zargi da ake yi masa.

A karshe alkalin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta wanke shi akan zargin da ta yi masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel