Albishir: Za a karawa masu yiwa kasa hidima allawus - DG NYSC

Albishir: Za a karawa masu yiwa kasa hidima allawus - DG NYSC

Shugaban NYSC mai kula da matasa masu hidimtawa kasa (NYSC) Manjo-Janar Sulaiman Kazaure ya ce za a yiwa masu yiwa kasa hidima karin allawus da zarar an kammala zartar da karin albashi mafi karanci da gwamnati tayi.

Kazauren ya yi wannan jawabin ne a yau Juma'a yayin da ya hallarci bikin rantsar da masu hidimar kasar guda 3,022 na Batch A a sansaninsu da ke Abuja. Ya ce NYSC tana jira ne gwamnati ta sanya hanu a kan kudirin karin albashin ya zama doka.

A kan batun fara tantance wadanda suka kammala karutun digiri a jami'o'in NOUN, Kazaure ya ce da zarar gwamnati ta bayar da umurnin a fara tantance su domin zuwa yiwa kasa hidimar za a fara ba tare da bata lokaci ba.

DUBA WANNAN: Zababun 'yan majalisan APC 16 a Sokoto sun ki zuwa karbar takardan shaidan cin zabe

Da duminsa: FG za ta karawa 'yan yiwa kasa hidima albashi - NYSC
Da duminsa: FG za ta karawa 'yan yiwa kasa hidima albashi - NYSC
Asali: Depositphotos

Ya kuma gargadi sabbin 'yan yiwa kasar hidimar su kasance masu nuna halaye na gari a yayin zamansu a sansanin kuma su guji shan miyagun kwayoyi.

Kazaure ya bukaci su kasance masu kishin kasarsu a duk inda aka tura su yin hidimar kana su kasance masu amfanar da garuruwan da aka tura su yin hidimar.

A wurin bikin bude sansanin masu yiwa kasa hidimar, Ministan Abuja, Alhaji Muhammad Bello da ya samu wakilcin shugaban ma'aikatar kudi, Hajiya Safiya Umar ya janyo hankalin masu yiwa kasa hidimar a kan karramawa da ake yiwa wadanda su kayi kwazo a cikinsu.

Ya kuma basu shawara su mayar da hankali wurin koyan sana'o'i na dogaro da kai da ake koyarwa a sansanin karkashin shirin Skills Acquisition and Entrepreneurial Development (SAED).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel