Kotu tayi fatali da bukatar soke zaben Adamawa

Kotu tayi fatali da bukatar soke zaben Adamawa

Wata babban kotu da ke zamanta a Yola tayi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam'iyyar Movement for Restoration and Defence of Democracy (MRDD), Rabaran Eric Theman ya shigar na neman a soke zaben gwamna da aka gudanar a jihar.

Theman ya kallubalanci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC inda ya ke bukatar a sake sabon zabe saboda an cire tambarin jam'iyyarsa a takardun kada kuri'a da akayi amfani da su a zaben.

Jastice Abdulaziz Waziri ya ce wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da hujja da ke nuna an cire tambarin jam'iyyarsa a takardan kada kuri'a yayin zaben.

DUBA WANNAN: Shugabancin majalisa: Buhari, gwamnoni da shugabannin APC sun lallashi Goje

Kotu tayi fatali da bukatar soke zaben Adamawa
Kotu tayi fatali da bukatar soke zaben Adamawa
Asali: Twitter

Hukumar INEC ta bayyana cewa zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba hakan ya zabi ranar 23 ga watan Maris domin gudanar da zaben raba gardama amma umurin kotu ta Jastis Waziri ya bayar ya sanya INEC ta dakatar da yin zaben raba gardamar.

Daga bisani dai anyi zaben raba gardamar a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris bayan Jastice Waziri ya janye umurnin dakatar da zaben.

Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Ahmadu Fintiri ne ya lashe zaben inda ya kayar da gwamna mai ci yanzu na jam'iyyar APC, Muhammadu Jibrilla.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel